34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Musu kan kungiyoyin kwallon kafa na Chelsea da Barcelona ya sanya aboki ya kashe abokin shi a Katsina

LabaraiMusu kan kungiyoyin kwallon kafa na Chelsea da Barcelona ya sanya aboki ya kashe abokin shi a Katsina

An gurfanar da wani dan shekara 18 mai suna Idris Yusif, a gaban babbar kotun majistare ta jihar Katsina, a bisa tuhumar sa da kashe wani Saifullahi Abdullah, a kan musun kwallon kafa.

A cewar jaridar Punch, Saifullahi mai shekaru 28 ya mutu ne bayan musu da suka yi akan wacce kungiyar kwallon kafa ce tafi wata, tsakanin Chelsea da Barcelona, inda daga baya, wannan musu ya rikide ya koma fada a tsakanin su, a ranar 12 ga watan Disambar shekara ta 2021, cikin karamar hukumar Danja dake jihar Katsina.

Mahaifin Saifullahi ya kai kara

Mahaifin mamacin, ya kai rahoton faruwar lamarin zuwa ga ofishin ‘yan sanda na Danja a ranar 20 ga watan Disambar 2021.

Yusif, wanda aka gurfanar dashi ranar Litinin a gaban babbar kotun majistare, ana tuhumar sa da laifin kisan kai. A karkashin sashi na 190, karamin sashi na(1) kamar yadda kundin tsarin doka na (penal code) ya tanada.

Da yake jawabi ga kotu, dan sanda mai gabatar da kara, Bello Lawan yace, Abdullah ya fadi kasa wanwar, a lokacin da suke rigimar tsakanin shi da wanda ake kara.

A asibiti Saifullahi ya rasu

Ya kara da cewa, an garzaya da mamacin asibiti, inda a can rai yayi halinsa.

A cewar rahoton farko:

“A ranar 18 ga watan Disambar shekarar 2021, da misalin karfe 3:30 na yamma, Saifullahi Abdullah yayi musu da kai, Idris Yusuf, dan shekara 18. A unguwar Hayan Asibiti dake Danja, akan wacce kungiyar kwallon kafa ce tafi wata karfi da kuma nagarta tsakanin Chelsea da Barcelona wadanda suke a kungiyoyin wasannin nahiyar turai. Wanda a sakamakon haka abin ya rikide ya zama fada wanda shi Saifullahi ya fadi magashiyan.

“Daga baya, aka garzaya da mamacin cibiyar kula da lafiya ta Danja (Danja comprehensive health centre ) aka kwantar da shi, inda daga baya kuma likita ya tabbatar da mutuwarsa “

Bayan sauraren koken dan sanda mai gabatar da kara, Fadile Dikko, alkalin kotun ta dage karar zuwa 7 ga watan Maris, 2022.

Sannan ta bada umarnin a ci gaba da tsare Yusuf a gidan kaso har zuwa ranar da aka daga shari’ar.

Dumbin bashi ya sa wani mutum ya kashe kan sa a jihar Kwara

An tsinci gawar wani mutum mai suna Olakunle Obaoye, mai shekaru 25, rataye a cikin daji a cikin ƙauyen Erinmope kusa da Ayedun da ke ƙaramar hukumar Oke Ero a jihar Kwara.

A cewar ‘yan’uwan mamacin, mutumin ya halakabkansa ne bisa dalilin kasa biyan ɗumbin bashin da mutane ke bin sa, Jaridar Punch ta ruwaito.

Mai magana da yawun hukumar NSCDC na jihar Kwara, Babawale Afolabi, ya bayyana yadda aka tsinci gawar mamacin a ranar Litinin cikin daji.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe