24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Gombe: Matar aure ta kai mijin ta kotu saboda ya garza mata cizo kuma ya na hana ta abinci

LabaraiGombe: Matar aure ta kai mijin ta kotu saboda ya garza mata cizo kuma ya na hana ta abinci

Wata matar aure a jihar Gmbe ta maka mijin ta a gaban kotu saboda cizon ta da ya ke tare da hana ta abinci da kuma cin zarafin ta.

Wata babbar kotun majistare da ke zamanta a Unguwar Idi a jihar Gombe, ta dage shari’ar da wata Lawiza Muazu ta gabatar.

Gombe: Matar aure ta kai mijin ta kotu saboda ya garza mata cizo kuma ya na hana ta abinci
Gombe: Matar aure ta kai mijin ta kotu saboda ya garza mata cizo kuma ya na hana ta abinci

Alkalin kotun, Garba Abubakar, ya dage sauraron karar zuwa ranar Litinin, 24 ga watan Janairu, 2022, domin bai wa matar mai suna Lawiza damar gabatar da shaidun ta.

Ta kai karar mijin ta mai suna Alhaji Muazu a gaban wata kotun yankin bisa zargin sa da cizon ta a lokacin da suke rikici.

Lawiza ta yi zargin cewa mijin kuma yakan yi mata dukan tsiya idan sun samu rashin fahimta.

A cewarta, “Rikicin da mu ka yi na baya-bayan nan shi ne lokacin da na ki dafa abinci a gidan. Matakin da na dauka ya faru ne sakamakon rashin samar da itace ko gawayi da shi ya yi.

“Lokacin da ya buge ni a karon farko, na koma gida, amma mahaifi na ya ce in koma. Daga baya miji na ya koma ya cije ni bayan duka. Ya kan ciji yatsuna don na ki dafa abinci.

Don haka ta roki kotu da ta raba auren ta da Muazu ta ce ba za ta iya kara hakuri da shi ba. Mijin matar ya ce matar ta ki yin girki
Da yake mayar da martani kan zargin, mijin Muazu ya musanta cewa ya ciji Lawiza da dukan tsiya.

Ya ce, “Ta ki yin girki har tsawon mako guda, wanda ya saba wa yarjejeniyar da aka yi mata na cewa mata na biyu za su ba da abinci a gidan a ranar girkinsu.”

Muazu ya bayyana cewa a dalilin haka matar Jummai ta ki bai wa Lawiza abincin da ta shirya.

“Don nuna rashin amincewar ta da rashin yi mata hidima, Lawiza ta kama ni ta na neman hakkin ta. Ta sa hannun ta cikin aljihu na ta na kokarin cire kudi da karfi. A sakamakon haka ne rigima ta shiga tsakanin mu amma ban taba cizon ta ba,” Muazu ya kara da cewa.

Miji ya bawa matar sa kwaya ya gayyato abokin aikin shi ya yi mata fyade akan idon shi

An yanke hukuncin zama gidan kaso na shekaru 3 ga wani mutum bayan yayi yunƙurin yin fyade ga matar abokin aikin sa, wacce mijinta ya gayyace shi domin yin wannan ɗanyen aiki.

An faɗi wannan labarin mara daɗin ji ne a kotun ƙolin kasar Singapore cikin wannan makon.

An sakaya sunayen su saboda tsabar munin laifukan da suka aikata.

A shekarar 2017, mutumin mai shekaru 47, ya amsa gayyatar da abokin aikin sa yayi masa ta zuwa gidan sa domin yin fyaɗe ga matar sa, Channel News Asia ta ruwaito.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe