34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Miji ya bawa matar sa kwaya ya gayyato abokin aikin shi ya yi mata fyade akan idon shi

LabaraiMiji ya bawa matar sa kwaya ya gayyato abokin aikin shi ya yi mata fyade akan idon shi

An yanke hukuncin zama gidan kaso na shekaru 3 ga wani mutum bayan yayi yunƙurin yin fyade ga matar abokin aikin sa, wacce mijinta ya gayyace shi domin yin wannan ɗanyen aiki.

An faɗi wannan labarin mara daɗin ji ne a kotun ƙolin kasar Singapore cikin wannan makon.

Wani mutum ya sanya wa matar sa abin maye sannan ya gayyato abokin aikin sa don yi mata fyade
Wani mutum ya sanya wa matar sa abin maye sannan ya gayyato abokin aikin sa don yi mata fyade

An sakaya sunayen su saboda tsabar munin laifukan da suka aikata.

A shekarar 2017, mutumin mai shekaru 47, ya amsa gayyatar da abokin aikin sa yayi masa ta zuwa gidan sa domin yin fyaɗe ga matar sa, Channel News Asia ta ruwaito.

Mutanen biyu sun san juna sosai bayan sun shafe lokaci mai tsawo suna aiki tare.

Sun ba matar kwayoyi da giya, sannan mijin yana kallo yayin da mutumin ya ci zarafin matar tasa.

Abin ban tsoron shi ne yadda yaran matar guda uku da mai aikin gidan suke kwance suna barci a wani ɗaki daban lokacin da lamarin ya auku.

Sai dai, mutumin wanda yayi yunƙurin yin fyaɗen, jikin sa ya dakatar da shi inda ya samu matsalar rashin tashin mazakutar sa wanda hakan ya sanya dole ya kasa ƙarasa aikata laifin.

Ya amsa laifin tuhumar da ake masa ta bada haɗin kai wajen aikata fyaɗe, inda bai kai ga aikatawa ba, sai kuma laifin keta haddi.

Matar ta samu ramuwar gayya, inda ta buƙaci mijin ta da abokin aikin sa, su rubuta takardar iƙirarin aikata laifin, wacce kuma su ka rubuta.

A cikin takardar, mutumin ya tabbatar da abinda ya auku, haɗi da abin kunyar da ya yi.

Daga bisani an gwada shi, inda aka gane cewa ya samu matsalar tashin mazakuta.

Mataimakiyar mai gudanar da bincike, Chee Ee Ling, ta buƙaci a yanke wa wanda take karewa hukuncin shekaru 2 da rabi a gidan kaso, wanda a watan Yunin shekarar 2018 aka yanke masa hukuncin watanni 12 kan sayar da littattafan batsa waɗanda ke cin mutuncin kamala, da kuma yin ta’ammali da bidiyoyin ɓatsa.

Akwai wasu mutane 6 masu hannu a cikin wannan aika-aikar, waɗanda za su gurfana a gaban kotu a cikin wata mai kamawa.

Ana sa ran huɗu daga ciki za su amsa tuhumar da ake yi mu su, ɗaya bai gama yanke shawara ba, yayin da na ƙarshe daga cikin su ya ki amsa tuhumar da ake masa ba, kamar yadda aka ruwaito.

Sharrin shaidan ne, Tsoho mai shekaru 65 da ya yi wa diyarsa fyade sau 4 ga hukuma

Sharrin shaidan ne, Tsoho mai shekaru 65 da ya yi wa diyarsa fyade sau 4 ga hukuma
Wanda ake zargin ya amsa laifinsa, inda yace sharrin shaidan ne, Daily Trust ta ruwaito.
Kwamandan NSCDC ya ce zasu ci gaba da bincike kuma matsawar suka gano ya aikata laifin sai ya fuskanci hukunci.
Ya kuma koka akan yadda ake cin zarafin yara mata a garuruwa inda yace ya kamata iyaye su kare hakkin yaransu ne ba su keta musu haddi ba.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe