27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Dumbin bashi ya sa wani mutum ya kashe kan sa a jihar Kwara

LabaraiDumbin bashi ya sa wani mutum ya kashe kan sa a jihar Kwara

Kashe kai – An tsinci gawar wani mutum mai suna Olakunle Obaoye, mai shekaru 25, rataye a cikin daji a cikin ƙauyen Erinmope kusa da Ayedun da ke ƙaramar hukumar Oke Ero a jihar Kwara.

A cewar ‘yan’uwan mamacin, mutumin ya halakabkansa ne bisa dalilin kasa biyan ɗumbin bashin da mutane ke bin sa, Jaridar Punch ta ruwaito.

Kwara Community
Dumbin bashi ya sa wani mutum ya kashe kan sa a jihar Kwara

Mai magana da yawun hukumar NSCDC na jihar Kwara, Babawale Afolabi, ya bayyana yadda aka tsinci gawar mamacin a ranar Litinin cikin daji.

Kamar yadda yace:

“A ranar Litinin, 17 ga watan Janairun 2022, kimanin ƙarfe 12 na rana, wani mutum mai suna Thomas Obaoye, mazaunin garin Ayedun, ya je ofishin mu na yankin domin sanar da jami’an mu mutuwar ɗan’uwan sa, Olakunle Obaoye, mai shekaru 25, wanda aka tsinci gawar sa a rataye saman bishiya, haka ya yi kama da kisan kai.

“Bayan samun wannan rahoton, jami’an NSCDC na gundumar Ayedun, sun garzaya zuwa inda al’amarin ya auku, sannan suka yi aiki tare da ‘yan’uwan mamacin wajen sauko da gawar tasa daga kan bishiyar.

Daga baya an miƙa gawar ga iyalin mamacin don su birne shi”

Babawale ya faɗa cewa an miƙa al’amarin ga hukumar ‘yan sanda domin cigaba da gudanar da bincike da ɗaukar matakan da su ka kamata.

Kano: Yadda wata mata ta danna wa wuyan ta fasasshen gilashi wanda ya yi ajalin ta

Kano – Ana zargin wata mata ‘yar anguwar Sheka da ke karkashin karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano da kashe kan ta da kan ta.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana yadda wata mata ta yi amfani da fasasshen gilashi na taga wanda ta dadara wa wuyan ta har sai da ran ta ya fita daga jikinta.

An samu bayanai akan yadda ta gartsa wa mahaifin ta cizo sannan ta datse dan yatsan ta wanda dama ya ke ciwo kafin ta halaka kan ta.

Dan uwan matar, Muhammad Sanusi ya shaida yadda ‘yar uwar tasa kafin ta halaka kan ta da kan ta ta yi fama da ciwon dan karkare na yatsa wanda ya dinga yi mata zugi.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe