24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Buhari bai bawa kowa umarnin cire tallafin man fetur ba – Sanata Ahmad Lawan

LabaraiBuhari bai bawa kowa umarnin cire tallafin man fetur ba - Sanata Ahmad Lawan

Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan, yace shugaban kasa Muhammadu Buhari babu wanda ya gayawa cewa za’a cire tallafin man fetur.

Ahmad Lawan din yace, shugaban kasar ya fada masa hakan ne yayin da ya kai masa ziyara, ranar Talata 18 ga watan Janairu, domin ya shaida masa damuwar yan Nageriya, akan jita-jitar cire tallafin man fetur din

Ministar kudi Hajiya Zainab Ahmad ce ta fada a watan Oktoban shekarar da ta gabata 2021, cewa gwamnatin tarayya tayi tanadin bada tallafin man fetur dinne kadai, a cikin watanni shidan farko a cikin Wannan sabuwar shekara.

Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan, ya bayyana cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari, bai umarci kowa ba a cikin gwamnatin sa, da ya aiwatar da cire tallafin man fetur.

Daily Trust, sun ruwaito cewa, Lawan din ya fadi hakanne bayan ganawa da shugaban kasar, a gidan gwamnati ranar Talata 18 ga watan Janairu a Abuja.

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan
Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan

Shugaban majalisar dattawan yace, ya gayawa shugaban kasar, damuwar da alummar yankin sa suke ciki, na halin matsin rayuwa, ciki harda zancen cire tallafin man fetur.

Ya kara da cewa, yayi wa shugaban kasar maganar ne saboda da yawa yan majalisa suna nuna damuwar su akan kiraye kirayen da akayi na a fito zanga-zanga akan maganar janye tallafin man fetur din.

Buhari bai gayawa kowa a cire tallafin man fetur ba- Ahmad Lawan

Da yake magana da yan jarida akan lamarin, Lawan din yace, yana farin cikin shaidawa yan Nageriya cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari, bai gayawa kowa ya cire tallafin man fetur ba.

Yace:

” Ah, lallai yan Nageriya zasu so jin abin da muka tattauna da shugaban kasa.

“Da yawa daga cikin mu, sun damu da kiraye-kirayen ‘yan kwanakinnan na a fito zanga-zanga, kuma da yawa daga cikin yan kasama sun damu. Al’ummar da suka zabemu duk sun damu akan maganar cewa gwamnatin tarayya zata janye tallafin man fetur. Mu a bangarenmu, na majalisu, masu wakiltar daukacin jama’ar Nageriya, wannan tilas ya zama lamari mai mahimmanci a garemu.

“Bamu dade da kammala hutun mu ba. Kuma yayin da muke tare da alummar mu a gida, da kuma hakiman gundumomin mu, mun ji radadin da suke ciki. Wannan yasa tilas na gana da mai girma shugaban kasa, a matsayin sa na shugaban gwamnatin mu, kuma shugaban kasar mu, domin mu tattauna wannan matsala da ta shafi duk yan kasa, kuma ina matukar shaidawa yan Nageriya cewa shugaban kasa bai umarci kowa a gwamnatin sa daya cire tallafin mai ba”

Idan za’a iya tunawa dai, ministar kudi, kasafi da tsare-tsare, Hajiya Zainab Ahmad ce, ta sanar, a watan Oktoban 2021 cewa, gwamnatin tarayya tayi tanadin bada tallafin man fetur ne kawai a watanni shidan farkon sabuwar shekarar nan, a kokarin gwamnatin na ganin kammala kakkabe hannun gwamnati a harkar man fetur din.

Tace:

“A kasafin mu na 2022, mun ware tallafin mai na rabin shekara ne kawai, a daya rabin kuma muna kokarin kammala kakkabe hannun gwamnati ne, a tsarin harkar man ; inda zamu maida hankali wajen tanadi, ga kudaden kasashen waje, da kuma ribar da zata shigo mana ta ma’aikatar mai da iskar gas.”

A sanya ido sosai, zai iya yiwuwa tuban muzuru ‘Yan Boko Haram ke yi – Sanata Ahmad Lawan

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya ce dole ‘yan Najeriya su sanya ido wajen karbar ‘yan Boko Haram da suka nuna cewa sun ajiye makamai sun tuba kuma suna neman gafara.

Da yake magana da manema labarai bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa ranar Litinin, Sanata Ahmad Lawan ya ce dole a sanya ido don tabbatar da cewa wadanda suka tuba din tuban gaskiya suka yi.

Helkwatar tsaro ta kasa ta ce sama da mutum 1,000 ne ‘yan Boko Haram din da suka hada manyan kwamandojin su da masu hada musu bama-bamai suka mika wuya ga rundunonin sojin Najeriya dake yankin Arewa maso Gabas.

Mutane da yawa sun nuna rashin goyon bayansu akan kokarin da gwamnatin tarayya take na koyawa tubabbun mayakan sana’a ta kuma sanya su cigaba da yawo cikin al’umma.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe