34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

‘Yan bindiga sun sace abokanan ango guda 7 da suka je daurin aure, sun bukaci a biya miliyan 60

Labarai'Yan bindiga sun sace abokanan ango guda 7 da suka je daurin aure, sun bukaci a biya miliyan 60
  • ‘Yan bindiga sunyi basaja da kayan sojoji inda sukai awon gaba da mutum bakwai da suke hanyar su ta zuwa daurin aure
  • Abun ya farune a ranar Asabar inda ‘yan bindigar suka sace mutanen akan Titi Isara da ke jihar ogun
  • ‘Yan bindigan sun bukaci a biya kudin fansa Naira Miliyan Sittin

Wasu ‘yan bindiga Da ba a san ko su waye bane, sanye da kakin sojoji sun yi awon gaba da wasu mutane 7 da suke hanyar su ta zuwa daurin aure a hanyar Isara da ke jihar Ogun dai dai karshen babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.

Jaridar PUNCH Metro  ta tattaro cewa wadanda abin ya shafa sun je wani daurin aure ne a garin Ibadan na jihar Oyo a ranar Asabar din da ta gabata, akan hanyar su ta komawa gidajen su da ke jihar Legas a ranar Lahadi mota daya daga cikin motocin tafiyan nasu ta lalace suna tsaka da tafiya.

Daya daga cikin wadanda abin ya rutsa da su, Folaha Akinsola, wanda ya zanta da Wakilin Jaridar Punch a ranar Litinin, ya bayyana cewa suna kokarin jawo motar da ta baci zuwa bakin hanya kawai masu garkuwan suka far musu.

Ya ce;

“Mun halarci wani daurin aure ne a Ibadan ranar Asabar, bayan daurin auren muka nemi daki a wanan wuri na Isara Washegari da misalin karfe 5:30 na safe muka hau shirin komawa jihar Legas. Tafiyar ta mu ta kasance a cikin ayari motocin mu guda uku da suka hada da Toyota Corolla guda biyu da Toyota Camry daya.

“Ni ina cikin Toyota Camry wacce ta ke a gaba sauran biyu suna bin mu a baya inda wata babbar mota ta sha gaban mu mukayi kokarin wuce ta. yayin da direbanmu ya wuce wannan motar, har mun dan yi tafiya mai nisa kafin nan mu ka fahimci cewar fa mun baro ‘yan uwan mu a baya.

“Sai muka juya baya muka koma don mu neme su. Mun dan yi tafiya kadan sannan muka same su a gefen hanya kusa da Isara. Daya daga cikin masu tuka motar mai suna Shola, ya ce motarsa ta samu matsala. Sai Muka yi dabaran yankan bel ɗin motarsa don muyi amfani da igiya wajen daure motar a jikin ta mu saboda mu samu saukin janta zuwa gaba sai kawai muka ga wasu mutane su huɗu dauke da makamai sun fito daga cikin daji sun yo kanmu”.

A cikin mutum bakwai da aka sace, Akinsola ya ce an sako mutum uku, a inda masu garkuwan suka bukaci a biya su kudi kimanin N60m domin fansan sauran mutum hudun da ke tsare.

Ya kara da cewa;

“Masu garkuwa sun fito ne sanye da kakin sojoji, inda suka tasa keyan mu zuwa cikin daji. Sun fi Su hudu, sauran suna daji ne. Sai da suka ƙwace kayayyaki mu kafin suka sake wasu daga cikin mu.

“Ina cikin mutanen da na yi sa’a aka sako ni inda suka ce mu je mu nemo kudi naira N15m Kudin fansan ko wani mutum daya daga cikin ‘yan uwan mu da suke tsare a hannun su. Don haka za mu tara jimilar kudi N60m kenan, don haka ne muke neman taimako a wurin al’ummar Najeriya saboda masu garkuwan sun ce za su hallaka su idan ba a samo wadannan kudaden ba.

“Bayan mun yi nasarar kubutowa daga hannunsu sai mu kai kokarin kira lambar 911. Muna kan hanyar komawa Ibadan sai muka ci karo da shingen wasu ’yan sandan, muka yi saurin kai musu rahoton lamarin. Amma sai suka nuna mana cewa lamarin ba huruminsu bane. Sai suka tura mu sashin ‘yan sanda na Isara.

“Daga baya mun kai rahoton lamarin inda shugaban jami’in ‘yan sandan wanan shiyya ya tura ‘yan sanda kusan 25 zuwa wurin da lamarin ya faru. Masu garkuwan suna ta aiko da bidiyoyin barazana na abokan mu dake hannun su.”

Akinsola ya bayyana sunayen wadanda abun ya faru da su kamar haka: Adeola Bude, John Segun, Demola, da kuma abokin aikin sa, Bude Shola.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe