27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Shugaban karamar hukuma ya fado daga kujera ya mutu, watanni 3 kacal da shiga ofis

LabaraiShugaban karamar hukuma ya fado daga kujera ya mutu, watanni 3 kacal da shiga ofis
  • Mutuwa ta dauke Emmanuel Leweh wata uku kacal da zama shugaban karamar Agwanga dake jihar Nasarawa
  • Ance ya rikito ne daga kujera, a yayin da yake tsaka da ganawa da kansilolinsa, a sakateriyar karamar hukumar, a ranar Litinin 10 ga watan Janairu
  • Daga baya shugaban karamar hukumar Agwanga din ya rasu a wani asibitin kudi a Abuja ranar Alhamis 13 ga watan Janairu

Shugaban karamar hukumar Agwanga, ta jihar Nasarawa ya mutu bayan shafe watanni uku kacal akan karagar mulki.

Daily Trust, sun ruwaito daga wata majiya da ba’a bayyana ba, cewa, marigayin ya fado ne daga kan kujera a yayin da yake tsakar ganawa da kansilolinsa, a sakateriyar karamar hukumar Agwanga dake jihar Nasarawa ranar Litinin 10 ga watan Janairu.

Legit.ng ma sun bayyana cewa marigayin ya fadi ne jim kadan bayan an gama taron, inda aka kai shi wani asibitin kudi dake babban birnin tarayya Abuja, ranar 13 ga watan Janairu.

Dan majalisar dokokin jihar Nasarawa, Samuel Tsebe, shine ya tabbatar da faruwar wannan mummunan al’amarin.

“Nayi rashin babban yaya na (Hon Emmanuel Joseph Leweh, shugaban karamar hukumar Agwanga) wanda mutuwa ta dauke a Wannan yinin, bayan yar gajeriyar jinya”.

Mamaci ya bawa iyalan shi wasiyar su mayarwa da gwamnatin jihar Yobe albashinsa na shekara 11

Iyalan marigayi Baba-Aji Mamman, wanda aka bayyana shi a matsayin tsohon ma’aikacin hukumar wutar lantarki ta jihar Yobe, sun ce sun mayar da wuri na gugar wuri har Naira miliyan 11 zuwa ga gwamnatin jihar, sakamakon rasuwar marigayin.

Iyalan sun bayyana hakan ne a ranar Larabar da ta gabata a wata sanarwa mai suna ‘Rokon gafara ga jama’a da ma’aikatar hukumar samar da wutar lantarki ta Damaturu, Jihar Yobe, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

A cewar jaridar, iyalan sun ce sun bi wasiyyar da shi marigayi Mamman din ya bayar ne, wanda aka samu labarin rasuwar sa a ranar 28 ga Maris, shekarar 2020.

An ce marigayin ya umurci ‘yan uwansa da su mayar wa gwamnatin jihar adadin albashin da yake karba na tsawon shekaru 11.

Iyalan marigayin sun ce yana lallabawa yaje aiki ne na ‘yan tsirarun kwanaki a kowa ne mako saboda halin tsufa da rashin lafiya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe