36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Ku kashe su kada ku bar ko daya da rai – Sakon Aregbesola ga jami’an tsaro kan ‘yan bindiga

LabaraiKu kashe su kada ku bar ko daya da rai - Sakon Aregbesola ga jami'an tsaro kan 'yan bindiga
  • An baiwa jami’an tsaron dake gadin gidajen gyaran hali na Nageriya da su harbe duk wanda yayi kokarin tserewa daga gidan
  • Ministan harkokin cikin gida Ogbeni Rauf Aregbesola , shine ya bada umarnin
  • Ya kara da cewa, duk jami’an dole ne su haramta duk wani yunkuri na shiga gurin. Inda yace duk wani yunkurin kutse, za’a daukeshi a matsayin yunkurin ballewa

Ministan harkokin cikin gida Ogbeni Rauf Aregbesola, a ranar Litinin, ya baiwa jami’an kula da gidajen gyaran hali umarnin harbe duk wanda yayi yunkurin tserewa daga gidajen.

Ya ayyana gidajen kyaran halin a matsayin yanki mai hadari, saboda haka duk wanda yayi yunkurin kai hari wurin baza’a barshi ya kai labari ba.

Aregbesola ya bada umarnin ne yayin da yake bayani ga babban jami’in gidan gyaran hali na Agodi. Yace bai kamata abar mutanen dake kai harehare gidajen gyaran hali domin kubutar da daurarru, a raye ba.

Yace dole ne jami’an su dakatarda duk wani mai kokarin keta tsaron gidan domin shiga, inda yace duk wani yunkurin hakan tamkar yunkurin balle gidanne kuma matakin zai hau kansa.

Aregbesolan yace, abu mafi mahimmanci shine, kare tsaron gidan ta yadda baza’a iya keta shiba. Wannan yanki ne mai hadari, hadarin gaske. Saboda haka, duk wanda yayi kokarin kutsawa ya shiga, yama riga ya mutu. Domin baza’a barshi ya kai labari ba.

Rauf Aregbesola, Ministan cikin gida
Rauf Aregbesola, Ministan cikin gida

“Ba zamu yarda ba, duk wani yunkuri na kutsawa cikin gidan haramtacce ne, saboda haka kada ku harbi wani domin ku raunatashi; a’a, ku harbeshi domin ku kasheshi. Wannan shine hakikanin misalin yadda kasa zata tabbatarda tsare al’ummarta.

Ya tabbatar wa da jami’an, cewa gwamnati zatayi iya kokari domin tabbatarda walwalarsu, a matsayin matakin farko, domin basu kwarin gwiwar aiwatar da aikin su.

“Za muyi iya kokari, domin tabbatar da nagartaccen aiki.

“Tilas na yabawa kokarinku, da ba’a sami rahoton bullar covid19 a wurinku ba.

“Wannan ya nuna kunsan aikin ku. Kuma bakwa barin duk wani nau’in kutse a wurinku.

“Dole ne ku iya dakatar da duk wani yunkurin kai hari ko wata mamaya. Sannan kuma duk wani nau’in yunkuri, za’a daukeshi a matsayin yunkurin.

Balle gidan yari: Sama da bursinoni 3000 sun tsere – Inji Aregbesola

Tun farko, Legit.ng sun bayyana cewa, Aregbesola ya tabbatarda tserewar bursinoni sama da 3000. Biyo bayan balle kurkuku a Nageriya, shekarar da ta wuce.

Da yake magana yayin wani tsaron manema Labaru, wanda jami’an yada labarai na ofishin Shugaban kasa suka shirya, a ranar Alhamis 11 ga watan Nuwamba 2021, a Abuja. Aregbesola din ya bayyana cewa bursinoni 4,860 ne suka tsere daga gidajen gyaran hali daban-daban a fadin Nageriya. Tun daga shekara ta 2020 zuwa yau. Amma daga cikin wancan adadin 984 kawai aka iya cafkowa aka dawo dasu.

Wannan yasa a kasar baki daya, bursinoni 3876 sun gudu daga gidajen yari.

Tsohon gwamnan Osun din jadda cewa hareharen baya-bayannan da ake kaiwa gidajen gyaran hali alamace da take nunawa cewa babu tsaro a Nageriya.

Babu bukatar nayi murabus dan an balle gidan yari: Inji Aregbesola

Haka kuma, yayi bayani, akan murabus dinsa daga mukanminsa na Ministan harkokin cikin gida, a sakamakon yawaitar hareharen da ake kaiwa gidajen gyaran hali, a fadin kasar.

Aregbesola yace bashi da dalilin yayi murabus din. Inda ya kara da cewa, babu bukatar hakan. Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba 8 ga watan Disamba, yayin da yake mai da martanin kiraye-kirayen da ake yi akan yayi murabus din,saboda yawan hareharen da ake yawan kaiwa gidajen gyaran halin. A rahoton Vanguard.

Kada ku dogara da gwamnati ta baku aikin yi, Aregbesola ga matasan Najeriya

Ministan cikin gida Rauf Aregbesola ya shawarci matasan Najeriya dasu fara abubuwa na dogaro da kai, wanda hakan zai taimaka musu ba tare da sai sun fita neman aiki ba.

Yayi gargadin cewa dogara da gwamnati ko kamfanunnuka su bawa mutane aiki ba zai kawo karshen matsalar rashin aikin yi ba a kasar.

Aregbesola ya bayyana hakane a wajen wani taron masu ruwa da tsaki da aka yi wanda aka sanya matasa da mata a ciki a yankin jihar Osun ta tsakiya a Osogbo, babban birnin jihar Osun.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe