29 C
Abuja
Saturday, December 3, 2022

Ina samun kai na cikin farin ciki a duk lokacin da nake tare da ke – Suleiman Isah ga matar shi Baturiya

LabaraiIna samun kai na cikin farin ciki a duk lokacin da nake tare da ke - Suleiman Isah ga matar shi Baturiya
  • Suleiman Isah ya bayyana yanda ya kasance cikin farin cikin kasancewa tare da matar shi Janine
  • Matashin ya bayyana farin cikin sane a ranar bikin zagayowar ranar haihuwar matarsa
  • Ya bayyana hakan ne a shafin sa na kafar sada zumunta wato Facebook

Matashin nan dan Najeriya mai shekaru 24 dan asalin jihar Kano, Suleiman Isah, ya wallafa rubutu a kafar sada zumunta na yanar gizo a kokarin da yake na taya matarsa Janine Sanchez Reimann murnar cika shekaru 48 a duniya.

Da yake bayyana hakan a shafin sa na Facebook, cikin nuna farin ciki Suleiman Isah ya daura kyawawan hotunansu shi da matar tasa wanda a hoton kadai za a fahimci yanda suke matukar kaunar junansu.

Inda yake bayyana ma duniya cewar fa matar sa daban take da sauran mata, tayi musu zarra, ya kara da cewa yana matukar sonta, kuma yana alfaharin kasancewan su tare.

“Ina taya matata murnar zagayowar ranar haihuwar ta, wacce soyayyarta ce take sani nishadi da farin ciki a ko yaushe. Sweetheart, ina alfaharin kasancewan mu tare. Ina Son Ki.” Ya rubuta.

Suleiman Isah, wanda ya cika shekaru 24 a watan Oktobar shekarar da ta gabata, ya auri ba’amurkiyar matarsa mai shekaru 48 inda aka yi gagarumin biki wanda aka gudanar a garin Kano a ranar 13 ga Disambar shekarar 2020, sun hadu shida matar tasa ne a shafin sada zumunta na Instagram.

Daurin auren ya samu halartar ‘yan Najeriya da dama ciki har da tsohon sanatan jihar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani.

Suleiman Isah da matarshi Janine
Suleiman Isah da matarshi Janine

A shekarar 2020 aka daura auren Suleiman Isah da Janine

Idan ba a manta ba a watan Janairun shekarar data gaba ta ne aka samu labarin ba’amurkiya Janine Sanchez Reimann ta biyo jirgi ta dira garin Kano dan kawai tazo ta hadu da masoyinta Suleiman Isah, zuwan na ta ya haddasa cece-kuce a kafafen sada zumunta inda mutane suke ganin cewa fa wannan mata tayi wa wannan yaron tsufa domin kuwa akwai tazarar shekaru 24 a tsakaninsu.

Hausawa sukace “SO”hana ganin laifi, shi dai wanan saurayi son da yake ma wannan mata ya hanashi ganin aibunta inda yafito ya bayyana wa duniya cewar fa shi yana son ta a haka, duk wanan cece-kuce da akeyi bai hana cigaba da shirye shiryen auren da Sulaiman yake shirin yi da baturiyar ba, wanda daurin auren ya samu halartar al’umma da dama.

Sai muce Allah ya kara dankon soyayya.

Ango ya saki Amaryar shi a wajen daurin aure, bayan an aika masa da hotunan tsiraicinta

An daura auren da aka rabu a wajen daurin aure sakamakon halayen banza da amaryar take da su a baya. Ma’auratan na cikin farin ciki da annushuwa a wajen bikinsu, sai aka bawa angon kyautar fure dauke da wani boyayyen sako.

An aika masa da takarda dauke da rubutu a jikin furen

Rubutun dake jikin takardar ya sanya mijin ya fara zargin halayen amaryar tashi, hakan ya sanya shi duba wasu hotuna da aka aiko masa da su.

Angon ya duba hotunan a wani kebantaccen daki

Wannan hotuna dai tsohon saurayin amaryar shi ne ya aiko masa da su, inda da yawa daga cikinsu na tsiraici ne.

Hotunan sunyi muni matuka, hakan ya sanya angon fushi sosai, inda a wajen ya yanke shawarar kawo karshen auren na su baki daya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe