36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Kano: Yadda wata mata ta danna wa wuyan ta fasasshen gilashi wanda ya yi ajalin ta

LabaraiKano: Yadda wata mata ta danna wa wuyan ta fasasshen gilashi wanda ya yi ajalin ta

Kano – Ana zargin wata mata ‘yar anguwar Sheka da ke karkashin karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano da kashe kan ta da kan ta.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana yadda wata mata ta yi amfani da fasasshen gilashi na taga wanda ta dadara wa wuyan ta har sai da ran ta ya fita daga jikinta.

201503120944120510
Kano: Yadda wata mata ta danna wa wuyan ta fasasshen gilashi wanda ya yi ajalin ta

An samu bayanai akan yadda ta gartsa wa mahaifin ta cizo sannan ta datse dan yatsan ta wanda dama ya ke ciwo kafin ta halaka kan ta.

Dan uwan matar, Muhammad Sanusi ya shaida yadda ‘yar uwar tasa kafin ta halaka kan ta da kan ta ta yi fama da ciwon dan karkare na yatsa wanda ya dinga yi mata zugi.

Sanusi ya ce sai da ta kai ga an rufe ta a wani daki na kwana biyar saboda ciwon ya sa ta koma kamar wata mara hankali.

A cewarsa a ranar da suka bude ta ta ragargaza gilashin tagar dakin da aka rufe ta a ciki sannan ta yi amfani da gilashin wurin yanka wuyanta.

Kusan mutane 5 kenan suka halaka kawunansu a jihar Kano, kuma da yawansu an alakanta matsalar da cutar kwakwalwa.

An samu wani matashi a ‘yan baya-bayan nan wanda ya halaka kan sa ta hanyar datse alaurar sa.

Yayin da ‘yan adaidaita sahu suka tafi yajin aiki, gwamnatin Kano ta fito da sabuwar hanyar sufuri

Gwamnatin jihar Kano za ta kaddamar da sabon tsarin sufuri da zirga zirga a cikin fadin jihar nan ba da jimawa ba.

Manajan daraktan hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano, Baffa Babba-Dan’agundi, shine ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan tsawaita yajin aikin da masu tuka a daidaita sahun suka shiga a jihar.

Ya ce:

“Gwamnati za ta fitar da sabon tsarin zirga zirga ne saboda muna son sanin yadda ake tafiyar da harkokin sufuri kamar yadda yake gudana a yanzu.

“Tuni dai shirye-shirye sun kan kama wajen ganin an samar da ababen hawa ga al’umar jihar.

Masu tuka a daidaita sahun sun tafi yajin aiki ne sakamakon bijiro da wani tsari da akayi na shigar da takardar izinin aiki. A inda gwamnatin jihar ta zabge kudin takardar izinin daga N100,000 zuwa N8,000, domin saukaka musu su samu damar biya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe