34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Ina da tabbacin cewa zan lashe zaben shugaban kasa a 2023 – Bola Tinubu

LabaraiIna da tabbacin cewa zan lashe zaben shugaban kasa a 2023 - Bola Tinubu

Bola Ahmad Tunibu ya bigi kirgin cewa zai kawarda duk wani kalubale da ka iya kawo masa cikas wajen samun nasara a zaben Shugaban kasa na shekara ta dubu biyu da ashirin da uku 2023.

Tunibun yayi Wannan bugun kirjinne a ranar Asabar 15 ga watan Janairu 2022 bayan ziyarar da ya kai Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Ya kara da cewa, yana da tabbacin shine zaiyi nasara a zaben Shugaban kasa mai zuwa, saboda gagarumin goyon bayan da yake dashi daga magoya bayansa.

Bola Ahmad Tunibu, na jamiyyar APC ya bigi kirjin cewa duk da kalubalen da yake fuskanta a takarar sa ta Shugaban kasa mai zuwa na shekara ta dubu biyu da ashirin da uku 2023 ; yana da tabbacin shine zaiyi nasara a karshe.

Jagoran APC na kasar, yayi wannan bayaninne a ranar Asabar 15 ga watan Janairu 2022, yayin ziyarar da ya kai wa tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja. A rahoton The Cable.

Tunibun yace, yana da kwarin gwiwa, duba da kalaman alasambarka, da kuma goyon bayan da yake samu daga manyan mutane, da kuma magoya baya. Wanda a cewarsa, abin karfafa gwiwa ne da baza’a iya misaltashiba. A cewar Daily Trust.

Tsohon gwamnan Legas din ya nuna cewa, ita kanta rayuwa fal take cike da kalubale kala-kala. Amma shi zai yi kokarin tunkarar kowanne irin kalubale ya ga bayansa.

Ga abin da yake cewa:

“Rayuwa cike take da kalubale, saboda haka dole ne ka tunkari kalubalen, domin kaga bayan su. Ina da tabbacin lallai zan kawadda duk wani kalubale dake mini barazana. Lallai zan tunkari dukkan kalubalen dake gabana. Kuma ina da kwarin gwiwar sharesu gaba daya.

“Martanin manyan mutane akan muradina na zama Shugaban kasa; martanine mai kyau, abin karfafa gwiwa, mara misaltuwa. Wannan ne abinda ya kara mini kaimin cewa mune zamu zamo masu nasara a garshen zaben.”

2023: Abinda yasa zanbar Nageriya idan har Tunibu ya lashe zaben Shugaban kasa, Inji wani babba a jamiyyar PDP

Haka kuma, mai girma, Chief Bode George, tsohon mataimakin jam’iyyar PDP, ya bayyana ra’ayinsa, akan muradin takarar Shugaban kasan na Tunibu.

Babban a jamiyyar PDP, yace, Tunibun bazai iya sarrafa albarkatun kasar Nageriya ba, saboda haka tun wuri, yan Nageriya susan irin mutumin da zasu zaba a 2023.

A wata kwarya-kwaryan hira da yayi da jaridar Vanguard, George din yace, bazai iya jure radadin kasancewar Tunibu a matsayin wanda zai dinga wakiltar Najeriya a kasashen waje ba idan ya zama shugaban kasan da zai gaji Buhari.

Na tabbata cewa zamu kawo karshen matsalar tsaro – Bola Tinubu

Bola Ahmad Tunibu yace, Nageriya ce zata yi nasara akan yaki da ‘yan fashin daji, masu garkuwa da mutane, masu kashe-kashen mutane, da duk wata matsalar tsaro.

Jagoran APC ya bayyana hakan ne a jihar Katsina, yayin da yaje gaisuwar mutuwa.

A fadarsa, Nageriya babbar kasace da tafi karfin yan ta’addan. Saboda haka gwamnatin tarayya zata yi duk mai yiwuwa wajen murkushe su.

Jagoran APC, Tunibun ya aikawa da yan Nageriya sakon kwarin gwiwa.

A cewarsa, Nageriya zata ga bayan yan fashin daji, masu garkuwa da mutane, masu kashe-kashen mutane, da duk wata matsalar tsaro da kasar ke fuskanta.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe