36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Na tabbata cewa zamu kawo karshen matsalar tsaro – Bola Tinubu

LabaraiNa tabbata cewa zamu kawo karshen matsalar tsaro - Bola Tinubu

Bola Ahmad Tunibu yace, Nageriya ce zata yi nasara akan yaki da ‘yan fashin daji, masu garkuwa da mutane, masu kashe-kashen mutane, da duk wata matsalar tsaro.

Jagoran APC ya bayyana hakan ne a jihar Katsina, yayin da yaje gaisuwar mutuwa.

A fadarsa, Nageriya babbar kasace da tafi karfin yan ta’addan. Saboda haka gwamnatin tarayya zata yi duk mai yiwuwa wajen murkushe su.

Jagoran APC, Tunibun ya aikawa da yan Nageriya sakon kwarin gwiwa.

A cewarsa, Nageriya zata ga bayan yan fashin daji, masu garkuwa da mutane, masu kashe-kashen mutane, da duk wata matsalar tsaro da kasar ke fuskanta.

Ya bayyana hakan ne yayin ta’aziyah da ya kaiwa gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari. Saboda kisan baya- bayannan da aka yiwa kwamashinansa na ma’aikatar kimiyya da fasaha, Dr Rabe Nasir. Kamar yadda PM News Reports suka bayyana.

Tunibun yace, Nageriya babbar kasace da tafi karfin masu tada kayar bayan. Saboda haka gwamnatin tarayya zata yi amfani da duk matakin da ya kama, domin kawar da su.

Yace:

“Katsina tana fuskantar yanayi mai wahala, a sakamakon matsalolin tsaro da suka dabaibayeta. Muyi hakuri, duk abinda ya sami dayan mu kamata yayi muji tamkar ya samemu ne.

Wajibine mu tashi tsaye domin mu taimaki kasar mu. Mu ja hankali ga zaman lafiya, mu kuma yi kokarin ganarda wadanda suke son ayyukan ta’addanci, garkuwa da mutane, da sauran miyagun ayyuka a cikinmu.

“Ina kira ga gwamnatin tarayya, a karkashin shugaba Muhammadu Buhari, a matsayin sa na shugaban rudunar sojojin Nageriya, da yayi amfani da duk wani karfi wajen kawar da wadannan mutanen.

Muna ji (radadin ) tare, kuma zamu ci gaba da addu’a ga gwamnatin Katsina da kuma duka ‘yan Katsina baki daya. Domin suyi nasara akan’ ‘yan ta’addan da suke kashe-kashen wadanda basu jiba basu ganiba.

Deji Adeyanju yayi watsi da muradin Bola Tunibu na takarar Shugaban kasa

Haka kuma, tun farko, Legit.ng sun bayyana cewa, Deji Adeyanju, dan rajin kare hakkin Dan Adam, da kuma kishin hadin kan yan Nageriya, yayi watsi da muradin takarar Tunibun ta Shugaban kasa.

Da yake martini kan muradin Tunibun, haifaffen jihar Kogin, Adeyanju, ya gargadi yan Nageriya da suyi hankali da tsohon gwamnan Legas din. Inda ya ayyana shi a matsayin dan rashawa.

Ya kara da cewa, Tunibun zai jinginar da kasarne, Kamar yadda yayi wa jihar Legas.

EFCC ta kama Manjo Janar din soji na bogi

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa, (EFCC ) yankin Legas, ta kama Bolarinwa Oluwasegun a bisa laifin sojan gona, a matsayin Janar din Soji na Najeriya.

A wani rahoto da hukumar ta EFCC ta wallafa a shafinta sun bayyana lamarin ne a shafinsu na Facebook a ranar Alhamis 13 ga watan Janairun shekarar 2022.

Rundunar EFCC ta jihar Legas ce ta kama shi

Rundunar hukumar EFCC ta jihar Legas, sune suka gano Janar din bogin tare da bankado almundahanar da ya tafka har ta kimanin kudi Naira miliyan dari biyu da saba’in (N270,000,000).

Wanda ake zargin, ya gabatar da bayanan karya ga masu korafi a kansa, wanda kamfanin tantance biyan kudade ne, inda yace musu, da shi da wani da ba’a bayyana ba; wai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tantance su domin a zabeshi a matsayin babban shugaban sojoji (chief of army staff).

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe