24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

An kama tsohon Sanata da hannu a kisan shugaban kasa

LabaraiAn kama tsohon Sanata da hannu a kisan shugaban kasa
  • An kama wani tsohon dan majalisar dattawan kasar Haiti wanda ake zargi da kisan shugaban kasar
  • Hukumomi a Jamaica sun kama Jean Joel Joseph, tsohon dan majalisan ne a yammacin Juma’a, 14 ga watan Janairu
  • Joseph dan siyasar kasar Haiti mai adawa da jam’iyyar Tet Kale ta marigayi tsohon shugaban kasar

An kama Jean Joel Joseph, tsohon dan majalisar dattawa na kasar Haiti wanda ake nema ruwa a jallo bisa zargin kisan shugaban kasar Jovenel Moïse a Jamaica. BBC ta ruwaito cewa hukumomin Jamaica a ranar Asabar, 15 ga watan Janairu, sun tabbatar da cewa sun kama Joseph ne a yammacin Juma’a, 14 ga watan Janairu.

Jami’in Constabulary Force dake Jamaica (JCF) a wata sanarwa sun bayyana cewa an kama Joseph ne tare da wasu mutane uku da ake zargin ‘yan uwansa ne kan laifin shige da fice. An bayyana cewa an kama joseph ne a wani gida a St. Elizabeth, wanda ke cikin wani karamin coci da ke kudu maso yammacin tsibirin.

A cewar majiyar ‘yan sandan Jamaica, Joseph yana tsare. ABC News ta ruwaito cewa kakakin ‘yan sanda Gary Desrosiers ya ki bayar cikake karin bayani game da kama shi da akayi.

Hukumomin kasar Haiti su ne suka tuntubi masu binciken a Jamaica wadanda suka lura cewa ana neman tsohon dan majalisar Haiti ne a matsayin wanda ake zargi da kashe shugaban kasar.

A baya dai jaridar Labarun Hausa ta kawo muku rahoton yadda kashe shugaban kasar Haiti a gidansa da ke Port-au-Prince babban birnin kasar.

Sanarwan kisan Moise ta fito ne a cikin wata sanarwa da ta fito daga wajen Firayim Ministan wucin gadi na kasar ta Haiti, Claude Joseph.

Claude Joseph ya bayyana cewa, an kai mummunan harin ne da sanyin safiyar ranar Laraba, 7 ga watan Yulin shekarar 2021.

Wannan dalili ya sanya jami’an tsaro a kasar Haiti ba suyi kasa a gwiwa ba wajen bankado mutanen da ake zargin suna da alaka da kisan shugaban kasar.

A cewar shugaban ‘yan sanda a Haiti, Léon Charles, jami’ai a ranar Laraba, 7 ga Yuli, 2021, sun yi nasarar kashe hudu daga cikin wadanda ake zargin tare da samun nasarar cafke mutum biyu. Charles ya sanar da cewa wadanda aka kaman wanda suke kwararrun ‘yan ta’adda ne a yanzu haka suna tsare a hannun ‘yan sanda.

EFCC ta kama Manjo Janar din soji na bogi

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa, (EFCC ) yankin Legas, ta kama Bolarinwa Oluwasegun a bisa laifin sojan gona, a matsayin Janar din Soji na Najeriya.

A wani rahoto da hukumar ta EFCC ta wallafa a shafinta sun bayyana lamarin ne a shafinsu na Facebook a ranar Alhamis 13 ga watan Janairun shekarar 2022.

Rundunar hukumar EFCC ta jihar Legas, sune suka gano Janar din bogin tare da bankado almundahanar da ya tafka har ta kimanin kudi Naira miliyan dari biyu da saba’in (N270,000,000).

Wanda ake zargin, ya gabatar da bayanan karya ga masu korafi a kansa, wanda kamfanin tantance biyan kudade ne, inda yace musu, da shi da wani da ba’a bayyana ba; wai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tantance su domin a zabeshi a matsayin babban shugaban sojoji (chief of army staff).

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe