23 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Zaben 2023: Cancanta za mu bi wajen zaɓar shugaban ƙasa -inji dattawan arewa

LabaraiZaben 2023: Cancanta za mu bi wajen zaɓar shugaban ƙasa -inji dattawan arewa

Ƙungiyar dattawan arewa ta tabbatar da cewa yankin arewa zai zaɓi ɗan takarar shugaban ƙasa wanda ya cancanta ne, ba tare da yin la’akari da yankin da ya fito ba, a babban zaben 2023 mai zuwa.

Ƙungiyar ta ci alwashin ba zata sake maimaita kuskuren zaɓar kowane irin ɗan takara ba, kamar yadda aka yi wurin zaben shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2015 bisa bin son zuciya, jaridar independent.ng ta ruwaito.

Ƙungiyar ta nuna rashin gamsuwarta da kamun ludayin salon mulkin shugaba Buhari, ba a yankin arewaci kawai ba, har a ilahirin yankunan ƙasar nan.

Muhammadu Buhari
Zaben 2023: Cancanta za mu bi wajen zaɓar shugaban ƙasa -inji dattawan arewa

Me dattawan arewa suka ce a kan shugabancin kasa?

Darektan watsa labarai da wayar da kai na ƙungiyar, Dr. Hakeem Baba-Ahmed shi ne ya bayyana hakan a wata zantawa da yayi da manema labarai bayan an kammala taron gamayyar ƙungiyoyin arewa a gidan Arewa House, Kaduna, ranar Asabar.

A cewarsa, ‘yan arewacin Najeriya da takwarorin su na kudu suna da damar tsayawa takarar neman shugabancin ƙasa a zaben 2023. Sai dai ya ƙara da cewa, yankin arewa zai zaɓi nagartaccen shugaba ne a 2023, ba tare da tunanin yankin da ya fito ba.

Baba-Ahmed ya ƙara da cewa, ba wani ɗan takara daga arewacin Najeriya da zai yi amfani da yankin a zaben 2023, inda yayi nuni da cewa haka yankin ya kare da abinda ya kira da “kuskuren zaben Buhari”.

Ya faɗi cewa, yaudarar arewa aka yi wajen zaɓar shugaba Buhari, bisa yarda da cewa ƙasa zata gyaru amma sai gashi akasin hakan aka samu. Ya bayyana yadda ƙasar nan ta taɓarɓare fiye da yadda shugaba Buhari ya amshi mulkinta a shekarar 2015.

Baba-Ahmed, wanda tsohon magatakarda ne a hukumar zabe ta ƙasa, ya ƙara da cewa:

“Duk wanda ya fito daga yankin arewa da wanda ya fito daga kudancin Najeriya ya na da damar tsayawa takara, sannan ya yakamata duk dan arewa ya yi wa kansa karatun ta-natsu wajen duba wanda zai zaɓa a 2023.

“Ba wani ɗan arewa da zai sake wasa da hankalin mu. Haka mu ka kare da zaben shugaba Buhari. Ba mu son sake maimaita wannan kuskuren.

“Idan har lallai sai ɗan arewa to dole ne yafi sauran yan takarar, wannan shi ne abin dubawa a wurin mu. Zama ɗan arewa kawai yayi kaɗan, dole ya fi duk wanda sauran yankunan Najeriya suka fitar nagarta kafin a tsayar da shi.

“Muna neman shugaba ɗan Najeriya ne. Za mu ji dadi idan ya fito daga arewacin Najeriya, amma dole ya kasance jama’an Najeriya ne su ka zaɓe shi, sannan yafi sauran ‘yan takarar nagarta. Wannan shine abinda mu ke buƙata.”

Ya bayyana mulkin shugaba Buhari a matsayin wanda ya gaza ta kowane fanni, kama daga taɓarɓarewar tsaro, cin hanci da rashawa da kuma karyewar tattalin arziki.

Shugaban Kasa Buhari Ya Ce Ya Yi Iyakar Iyawar kokarinsa ga ‘yan Najeriya

https://www.labarunhausa.com/6291/shugaban-kasa-buhari-ya-ce-ya-yi-iyakar-iyawar-kokarinsa-ga-yan-najeriya/Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya yi iyakacin kokarinsa ga kasar Najeriya, inda yake fatan ‘yan Najeriya za su yi dubi ga kokarinsa bayan ya sauka daga kan mulki.

A wata zantawa da yayi da Gidan talabijin na kasa wato NTA a ranar Alhamis 6 ga watan Janairun 2022, shugaban yace ba ya sa ran samun jinjinar yabo daga yan Najeriya.
Shugaban ya jaddada cewa ya san ba karamin kokari yayi ba saboda yanayin da ya tsinci kasar a ciki lokacin da ya karbi ragamar mulki.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe