27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Malamin makaranta da yasa matarsa ta zubar da ciki har sau 5, ya fito yana neman taimakon al’umma

LabaraiMalamin makaranta da yasa matarsa ta zubar da ciki har sau 5, ya fito yana neman taimakon al'umma
  • Mista Abdullahi Yusuf, tsohon malamin makarantar Sakandare da ke Kwara suna cikin jarabawar rayuwa shi da matarsa
  • Matarshi Rukayat mai shekaru 34 na neman agajin dashen koda
  • A kowacce rana tana karban karin jini sau biyu zuwa uku wanda hakan ya janyo duk wani asusun da ‘yan uwa suka yi ya kare

Da yake labartawa North Central Trust ya ce sun yi aure tun shekarar 2013, ’yarinya daya kawai suka haifa a dalilin zubar da duk wani ciki da matar ta samu,sun yi hakan har sau biyar saboda yanayin wahala da take shiga in ta samu cikin.

A cewarsa, lamarin ya samo asali ne tun lokacin da matar ta kamu da matsanancin hawan jini a lokacin da take dauke da juna biyu.

Ya ce:

“Mun yi aure a shekarar 2013 amma ‘ya daya kawai muka haifi wanda a yanzu haka shekarar ta takwas. Tana fama da matsalar hawan jini wanda yake hawa har 200 kuma hakan yana faruwane a duk lokacin da ta samu cikin da ya kai wata hudu ko biyar a dalilin hakan ne muka salwantar da ciki har sau biyar don ceto rayuwarta. Akwai ciki daya ya shafe kusan wata bakwai a jikinta kafin ya fita, wanda hakan sai da ya janyo ta kusa rasa ranta.

“Har takai ga, likitoci sun danganta, lamarin da fibroi. Inda aka tura mu wani asibiti mai zaman kansa inda suka nemi kudin aikin tiyata kimanin Naira 150,000.

“A matsayina na malamin makaranta mai zaman kansa, ba nida hanyar samun wannan kudade. Sai muka chanza asibiti inda muka ziyarci cibiyoyin lafiya daban daban, inda aka gaya mana cewa tana da hawan jini mai tsanani.

“Zuwan mu, Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilorin (UITH) a nan ne labari ya canza inda sashin Nephrology ta gano tana fama da cutar koda kuma suka ba da shawarar mu yi dashe saboda ita kadai ce mafita ga matsalar ta.

“Likitan da kansa ya bani shawarar cewa wanan jinyan ta fi karfin aljihu na sai aka bani shawaran in fito in nemi taimako’, in ji shi.

Abdullahi, wanda ya nemi tallafin kudi daga dukkan ‘yan Najeriya akan su taimaka masa su dauki nauyin dashen kodan matarsa, ya ce yanzu shekara guda matarsa na kwance jiki ya yi tsanani har ta kai ga da kyar ta ke iya magana.

“Jinyar da take fama dashi duk wasu kudaden da muke dashi ni da yan uwana, da sauran abokan arziki duk sun kare, akalla muna kashe Naira 106,000 a kowani sati wajen wanke mata kodan da kuma magunguna. Yanzu duk wani dabara da taimako sun gaza baza mu iya cigaba ba”.

Ya ci gaba da cewa matarsa na karbar ledar jini 2 zuwa 3 a kowacce rana inda a duk mako ana kashe kimanin Naira 120,000.

“Da farko dai don samun saukin kashe kudi ni da sauran ’yan uwa muna bada gudummawar jinin mu ana diba amma sai aka dakatar da mu saboda hakan na iya zama illa ga lafiyar mu kuma ma dole mu nemo kudin jinya.

“A yanzu haka sau biyu a kowani sati ake wanke mata koda, jimillar kudin da ake nema ya kai kimanin Naira miliyan 15 hade da magungunan da za a bata bayan anyi dashen.

“Wadanan kudade sun fi karfin danginmu da sauran abokan arziki ba za mu iya biya ba. Duk kudaden mu sun kare. Muna rokon Allah SWT ya bawa ‘yan Najeriya ikon ceto rayuwar matata.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe