22.1 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Ƴan bindiga sun halaka rayuka 2, kallafa sabon haraji a jihar Katsina

LabaraiƳan bindiga sun halaka rayuka 2, kallafa sabon haraji a jihar Katsina

Ƴan bindiga sun sanya harajin dubu goma N10,000 ga masu aikin haƙar zinare domin cigaba da gudanar da ayyukansu ba tare da katsalandan ba a ƙaramar hukumar Jibia da ke jihar Katsina.

A ƙauyen Bakin Korama ne ake hakar zinaren da ke cikin garin Magama wanda ya ke a bakin iyaka da Nijar.

Mazaunan garin sun bayyana cewa akwai ƙananun wuraren sarrafa zinare a wajen aƙalla guda 70, wanda aka buɗe sati biyu da su ka gabata.

Nigerian Bandits 1
‘Yan bindiga sun sace ‘yan kasuwa da dama a hanyar Kaduna

An gano cewa ƴan bindigan sun sanya harajin ne wa ma’aikatan, bayan sun kai samame a wurin ranar Alhamis da daddare, inda suka hallaka biyu daga cikin su.

Kamar yadda mazaunan garin su ka bayyana, harin ya fara ne da misalin karfe 8 na dare, inda ya shafe awanni biyu yana gudana.

Wasu mutane biyar daga cikin ma’aikatan sun samu raunuka a yayin harin, sannan ‘yan bindigan su ka yi awon gaba da ma’aikata 11 daga wurin.

Shugaban ƙungiyar masu sarrafa ma’adanai ta jihar Katsina, Tasiu Abdullahi, ya tabbatar da aukuwar al’amarin.

Ya bayyana cewa ƴan bindigan sun sako ɗaya daga cikin ma’aikatan. Sun sako shi inda su ka ba shi sakon wasikar da ke ƙunshe da batun kallafa harajin.

Abdullahi ya bayyana cewa,

“A ranar Alhamis ƴan bindiga sun kawo hari da misalin ƙarfe 8:10 na dare. Sun shigo ne ta hanyar wani rafi mai makwabtaka da mu. Su na isowa su ka fara amsar kuɗaɗe a hannun mutane bayan wani yaro ya sanar da isowar su. Sun halaka mutanen mu guda biyu, sun raunana mutane 5, sannan su ka tafi da mutane 11.

“Daga baya na samu rahoton cewa, ɗaya daga cikin waɗanda su ka ɗauke, ya dawo tare da sakon ‘yan bingidan na wata rubutacciyar wasiƙa cewa, harin somin taɓi ne, su na buƙatar haɗin kan mu wajen tabbatar da bin tsare-tsaren su a ko yaushe.

“Tsarin na su shi ne, ko wanne wurin aiki zai haɗa gudunmawar N10,000. Sun kuma bayyana cewa akwai mutane 11 a hannun su.”

Mai magana da yawun hukumar ƴan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da aukuwar al’amarin, inda ya ƙara da cewa ana gudanar da bincike.

“Tabbas ƴan bindiga sun kai hari a wajen aikin ma’adanan, inda su ka hallaka mutane 2, sannan su ka raunana wasu daga ciki waɗanda daga baya aka kai su asibiti domin duba lafiyar su. Mun fara gudanar da bincike kan haƙiƙanin abinda ƴan bindigan su ke muradi.”

Ƴan bindiga sun sace Hakimi, ƴan ƙasar waje 2 da mutane 9 a jihar Zamfara

Ƴan bindiga sun sace Hakimi, ƴan ƙasar waje 2 da mutane 9 a jihar Zamfara.

Ƙasa da kwanaki bakwai bayan ƴan bindiga sun ƙona kauyuka biyar a wani mummunan harin da suka kashe aƙalla mutane 200, yan bindigan sun ƙara ɗauke mutane 12 a wani sabon harin da su ka kai a jihar Zamfara.

Premium Times ta ruwaito yadda ‘ƴan bindigan su ka hallaka mutane 200 a kananun hukumomin Anka da Bukkuyum na jihar ta Zamfara a satin da ya wuce.

Shugaban majalisar ɗinkin duniya da shugaba Muhammadu Buhari sun yi Allah wadai da wadannan hare-haren takardun da su ka fitar daban-daban.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe