36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Mu na so sojoji su kawo karshen ‘yan bindiga kafin lokacin damina – Gwamnonin Arewa

LabaraiMu na so sojoji su kawo karshen 'yan bindiga kafin lokacin damina - Gwamnonin Arewa

Kwanaki kadan bayan bayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda, gwamnonin Arewa sun nuna bukatar sojojin Najeriya su kawo karshen ‘yan ta’addar kafin lokacin damina.

Shugaban kungiyar gwamnonin na Arewa, gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, shine ya bayyana haka ga manema labarai jiya a Abuja, bayan ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shi dake Villa.

A cewar shi, yankin Arewa yanki ne na noma saboda haka suna so al’umma su koma gonakin su, saboda dama rashin tsaro ne yake hana su zuwa gonakin na su.

Haka kuma ya nuna damuwa kan cigaba da samun matsalar garkuwa da mutane da ake yi a jihar sa dama yankin Arewa baki daya.

Simon Lalong - Shugaban Gwamnonin Arewa
Simon Lalong – Shugaban Gwamnonin Arewa

Gwamnatin tarayya ta bayyana su a matsayin ‘yan ta’adda

Ya ce:

“Wani abu game da hakan shine wasu daga cikin ‘yan bindigar har yanzu sun rage, kuma idan kuka yi duba gwamnatin tarayya tuni ta bayyana su a matsayin ‘yan ta’adda, saboda haka yanzu sojoji za su yi aiki da karfin su.

“Wannan sune matsalolin da muka yi magana a kan su a taron da muka gabatar a Kaduna. Saboda haka tuni mun riga mun fara gani, kuma mun fara shiri a Arewa don ganin irin wannan mataki.

“Mu tashi duka muyi abinda zai saka a farkon wannan shekarar, mutane za su fara samun kwarin guiwar cewa zaman lafiya zai dawo a kowanne yanki na Arewacin Najeriya, saboda muna so muga canji kafin zuwa lokacin damina

Yadda za a hada kan jami’an tsaro da ‘yan sa kai da kuma Sarakunan Gargajiya

“Wannan sune kadan daga cikin abubuwan, sai kuma magana kan hadin guiwa tsakanin jami’an tsaro da ‘yan sa kai, da kuma matsalar garkuwa da mutane da ta zama ruwan dare a yanzu.

” Abu na karshe shine sanya Sarakunan Gargajiya a ciki. Tuni mun riga mun aika da takarda zuwa ga majalisar dokoki, kuma za mu bi kanu a matsayin kungiyar gwamnonin Arewa domin tabbatar da cewa an sanya hannu akan wannan doka da za ta sanya Sarakunan Gargajiya su bawa gwamnati hadin kai wajen kawo karshen matsalar tsaro a jihohin,” cewar shi.

A karshe dai gwamnatin tarayya ta bayyana su Bello Turji a matsayin ‘yan ta’adda

A karshe dai gwamnatin tarayya ta ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda bayan shafe lokaci mai tsawo suna tashin hankula ga al’ummar Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF) kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya umarci kotu da ta yanke hukunci baiwa gwamnati umarni da ta ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda.

Haka kuma, gidan jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa a ranar Alhamis, 25 ga watan Nuwamba, 2021 mai shari’a Taiwo Taiwo na babbar kotun tarayya dake Abuja, shi ne ya amince da bukatar da gwamnatin tarayya ta gabatar na neman izinin ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Legit.ng

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe