27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

An kama dan kasar Indiya da yake sayar da mata Musulmai a kafar sadarwa

LabaraiAn kama dan kasar Indiya da yake sayar da mata Musulmai a kafar sadarwa
  • Hukumar ‘Yan sandan kasar Indiya sun cafke wani Vishal Jha, mutumin da ya sanya hoton wata Musulma a kasuwa
  • Vishal Jha ya sanya hoton wata mata a yanar gizo da sunan haja a kasuwa idan za a samu mai siya
  • ‘Yan sanda kasar Indiya sukai charaf suka cafke shi domin sanin Dalilin sa na yin haka inda ake tuhumar su tare da wata mata da ake tunanin abokiyar huldar sa ce.

An yi ram da wani mutum dan kasar Indiya wanda ya yada hoton wata Musulma domin siyarwa akan wata manhaja mai suna Bulli Bai.

‘Yan sandan kasar Indiyan sun sake cafke wata mata ‘yar Garin Uttarakhand wacce ake tuhumarta akan aikata wannan aika aikar.

person behind bulli bai app arrested by indian police
An kama dan kasar Indiya da yake sayar da mata Musulmai a kafar sadarwa


Wanda ake Tuhuma Mai Suna Vishal Jha, an cafke shi ne a Bengaluru kafin daga baya, aka mai da shi Mumbai a ranar 3 ga Janairu, 2022, yanzu haka yana tsare ana bincikarsa. Za a ci gaba da tsare sa a hannun ‘yan sanda har zuwa ranar 10 ga Janairu, 2022.

Har ila yau, matar da aka cafken tana nan a tsare ana gudanar da bincike a kanta. An kama ta ne bisa dalilin tarayyar ta da Vishal Jha.

Idan ba a manta ba, kwanakin baya Gidan Jaridar LabarunHausa ta labarto mana cewa hukumar kasar Indiya ta tuhuma wani kamfanin manhaja mai Suna” sulli Deals, wanda kalmar “sulli” kalma ce ta batanci, wanda ake amfani da manhajar wajen dora hotunan mata musulmai domin tallata su.

Hakan ya na faruwa ne ba tare da yardar su da amincewar su ba. Wanda hakan ya janyo hukumar ‘yan sandan kasar shiga lamarin inda suka bukaci karin bayani daga kamfanin.

Ma’aikatar mata ta,jihar da ke Delhi (DCW), ita ce ta mika wannan korafi ga hukumar ‘yan sandan domin ganin an dauki kwakwaran mataki game da wannan lamari, kuma ma’aikatar ta bukaci kwakwaran bayani ga me da lamarin.

A bisa faruwan wannan lamarin ne aka fitar da wani rahoton sashi na 354-A na kundin tsari kasar Indiya inda yayi magana akan cin zarafi.

Rahoton ya samu kyakyawan matsuguni har ta kai ga masa rajista, saboda korafin da aka yi wa hukumar yaki da laifukan yanar gizo, wanda hakan yana da alaka mai kusanci da manhajar “Sulli Deals”.

A cikin hotunan da aka saka, harda hotunan wasu manyan ‘yan jaridar kasar Indiya, tare da wasu ‘yan kasashen ketare.

A yanzu haka dai an yi nasarar goge wannan manhaja bisa dalilin yawan korafe-korafe da aka yi, cikin matan da aka wallafa hotunan su akwai wadanda suka bukaci da a bi musu hakkin cin musu zarafi da aka yi.

Budurwa ta kashe kanta bayan an wallafa bidiyon ta na tsiraici a shafukan sadarwa

A ƙasar Egypt wato Masar wata matashiyar budurwa ta halaka kan ta har lahira bayan hotunan tsiraicin ta sun karaɗe shafukan sada zumunta.

Tuni ƴan sanda suka damƙe wasu matasa guda biyu bisa zargin su da sa hannu dumu-dumu fcikin lamarin bayan mutuwar matashiyar yarinyar.

Yarinyar mai suna Bassant Khalid ta hallaka kan ta har lahira ne bayan hotunan tsiraicin nata da ake zargin cewa matasan da hadawa, sun dinga yawo a shafukan sada zumunta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe