27.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

An harbe jarumar fim har lahira yayin da tauraruwar ta ke kan haskawa

LabaraiKannywoodAn harbe jarumar fim har lahira yayin da tauraruwar ta ke kan haskawa

Yan bindiga sun harbe wata jarumar fim ta kamfanin fina-finai na Nollywood wadda aka fi sani da Ngozi Chiemeke, a ranar 8 ga watan Disambar shekarar 2021.

A cikin rahotannin da aka samu kan lamarin, sunce kisan ya faru ne a titin deeper life dake garin Boji-Boji Owa a karamar hukumar Ikar Arewa maso Yamma ta Jihar Delta.

An kashe jarumar fim din a wajen sana’arta ta POS

A rahoton da Mujallar Fim ta fitar, ta gano cewa an kashe jarumar wacce take kan ganiyar tashenta, a fina-finan Nollywood, a cikin shagon da take sana’arta ta shiga da fitar kudade, wato POS.

Yan unguwar da abin ya faru a kusa dasu, sunce, sunji karar rashin bindiga, amma koda suka rugo don su kawo dauki, basu tarar da kowa a wajen ba.

Babu wanda ya san abin da yasa aka yi kisan, domin har ya zuwa lokacin da aka dauketa daga wurin, babu wata shaida da zata nuna alamun wadanda keda hannu wajen wannan aika-aikar.

jarumar fim
Jarumar fim Ngozi Chiemeke

Mutane sun shiga rudani sakamakon kisan jarumar

Kisan jarumar, ya haifar da gagarumin rudani a cikin jama’ar garin, abin da yasa suka rika jinjina kisan gillar da aka yima jarumar, inda aka dauketa aka kaita dakin ajiye gawa domin cigaba da bincike.

A Jawabin jami’in yada labarai na hukumar ‘yan sandan jihar ta Delta, DSP Bright Edafe, ya bayyanawa manema labarai cewa tabbas labarin kisan jarumar ya iske rundunar tasu, inda ya tabbatar da cewa,

“Wasu maza da ba’a san ko su waye ba sune suka hallaka matashiyar jarumar. Amma sun fara fadada bincike domin kamo duk masu hannu akan kisan matashiyar jarumar dan gurfanar dasu a gaban shari’ah”.

‘Yan bindiga sun kashe mutum 13, sun yi garkuwa da 46 a Kaduna

A wani labari da jaridar Labarun Hausa ta kawo muku kuma, wasu ‘yan bindiga sun hallaka mutum sha uku a Kaduna da Taraba, tare da yin garkuwa da mutane 46, inda mutum 18 suka fito daga gida daya…

Yankin da al’amarin ya afku sun hada da unguwar Zalla Udawa da ke karamar hukumar Chikun inda aka kashe mutum daya tare da yin garkuwa da mutane 18 duka ‘yan gida daya.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:30 na safiyar Lahadi a lokacin da ‘yan bindigan suka dira a kauyen da ke kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Dagacin garin Udawa, Muhammed Umaru, shine ya bayyanawa Gidan Jaridar Daily Trust sunan Marigayin mai suna Bala Jaja.

Cikin wadanda akayi awon gaba da su akwai matan aure, tsofaffi da kuma ‘yan mata.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe