24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

A karshe dai gwamnatin tarayya ta bayyana su Bello Turji a matsayin ‘yan ta’adda

LabaraiA karshe dai gwamnatin tarayya ta bayyana su Bello Turji a matsayin 'yan ta'adda
  • A ranar Laraba 5 ga watan Janairu ne aka aka yanka ragon suna ga ‘yan bindigar da ke ta’addanci a yankin Arewacin Najeriya a matsayin ‘yan ta’adda
  • Hakan ya biyo baya ne bayan yanke hukunci da kotu ta yi wanda Ministan Shari’a Abubakar Malami shi ya umarci gwamnati da ta ayyana ’yan bindigan a matsayin ‘yan ta’adda
  • ‘Yan Najeriya sun yi ta kokarin kira ga gwamnati da ta ayyana ‘yan bindigar a matsayin ‘yan ta’adda sakamakon munanan hare-haren da suke kai wa mazauna kasar da ba su ji ba ba su gani ba

A karshe dai gwamnatin tarayya ta ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda bayan shafe lokaci mai tsawo suna tashin hankula ga al’ummar Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF) kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya umarci kotu da ta yanke hukunci baiwa gwamnati umarni da ta ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda.

Haka kuma, gidan jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa a ranar Alhamis, 25 ga watan Nuwamba, 2021 mai shari’a Taiwo Taiwo na babbar kotun tarayya dake Abuja, shi ne ya amince da bukatar da gwamnatin tarayya ta gabatar na neman izinin ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda.

Bangarorin da ta’addanci ya fi karfi sun hada da shiyyar Arewa maso Yamma, musamman jihohin Zamfara, Katsina, Sokoto da kuma Kaduna.

Sannan suka gangara yankin Arewa ta tsakiya inda suka mamaye sassa daban-daban da kuma sauran jihohin kasar.

‘Yan bindigan sun hallaka daruruwan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, tare da garkuwa da wasu da dama wanda suka hada da mata, yara, da ‘yan makaranta, inda wasu har yanzu suna hannunsu,

A baya dai Jaridar Labarun Hausa ta ruwaito cewa Babban Malamin Addini nan Sheikh Ahmad Gumi ya mayar da martani kan matakin da babbar kotun tarayya ta yanke na kokarin ganin an ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda.

Shehin Malamin ya bayyana cewa kiransu da ‘yan ta’adda ba zai sauya komai ba. Malamin na Kaduna a cikin wata sanarwa da Malam Tukur Mamu, mai magana da yawunsa kan harkokin yada labarai da Dan-Iyan Fika suka fitar ya bayyana cewa tun kafin bayyana ‘yan bindigar a matsayin ‘yan ta’addan dama can kallon ‘yan ta’addan ake musu.

Kungiyar CAN ta ce Sheikh Gumi na da hannu kan abubuwan da ‘yan bindiga ke yi

Duk da cigaba da samun matsalolin masu tada kayar baya, masu garkuwa da mutane da kuma abubuwan ta’addanci a Najeriya, kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta zargi Sheikh Ahmed Gumi da kara tunzura ‘yan bindiga akan abubuwan da suke yi .

Shugaban kungiyar ta reshen jihar Imo, Rev. Eches Divine, shine ya yi wannan zargi a wata hira da yayi da manema labarai a Abuja.

Eches ya shawarci gwamnati da ta lura da Malamin wanda maganganun shi suke kara tunzurawa da kuma karawa ‘yan bindiga karfin guiwa, kuma yake goyon bayan abinda suke yi a Arewacin Najeriya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Legit.ng

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe