23 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Ƴan sa kai sun kashe mutum 11 masu bai wa ‘yan bindiga bayanan sirri a Zamfara

LabaraiƳan sa kai sun kashe mutum 11 masu bai wa 'yan bindiga bayanan sirri a Zamfara

A ƙalla mutane 11 ne ƴan sa kai suka kashe bisa zarginsu da kai bayanan sirri ga ‘yan bindigar daji. Ƴan sa kan sun kashe wannan dandazon mutanen ne na masu fitar da bayanan na sirri ga ƴan bindigar dajin bayan kama su da suka yi a ƴan kwanakin nan.

Kamar yadda Jaridar Daily Trust ta bayyana a shafin ta, mutum bakwai daga cikin masu fitar da bayanan sirrin an kashe su ne a garin Gada dake ƙaramar hukumar Bungɗu, a Jihar Zamfara.

Gunmen Edo
Ƴan sa kai sun kashe mutum 11 masu bai wa ‘yan bindiga bayanan sirri a Zamfara

Bugu da ƙari, huɗu daga cikinsu wadanda suka haɗa da mace ɗaya mai suna Dabo Bokanya, an kashesu ne a kasuwar wayoyi ne dake garin Ƙaura Namoda duk a jihar Zamfara, wanda alkalumma suka nuna kisan mutum goma sha ɗaya kenan.
Hakazalika, Jaridar Independent ta ƙara da cewa, al’amarin ya faru ne a daidai lokacin da ƴan sa kan suka yi wa mutanen ƙawanya a kasuwar wayoyin.

Ku Bayyana Shaidar Kun Kashe Shugabannin ‘Yan Bindiga, Gumi ga Sojojin Najeriya

Shahararren Malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya buƙaci Sojojin Najeriya dasu gabatar da wasu shaidu da zasu tabbatar da cewa sun kashe wasu daga cikin gawurtattaun ‘yan bindigar daji biyu a dajin Zamfara a makon da ya gabata.

Shehin malami Gumi ya kara jaddada cewa, babban abinda zai sa a yii nasarar kawo ƙarshen wadannan ƴan ta’adda shi ne a zauna da su a yi sasanci, kamar yadda ya sha faɗa a baya.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe