24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Aiki ga mai kare ka: Za mu kone duka dazukan da ‘yan bindiga ke ciki – El-Rufai

LabaraiAiki ga mai kare ka: Za mu kone duka dazukan da 'yan bindiga ke ciki - El-Rufai
  • Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa duka za a kawo karshen ‘yan bindiga ta hanyar yi musu ruwan bama-bamai a kone dazukan da suke ciki baki daya
  • Gwamnan ya ce ya san tabbas za a tafka asara, amma dai kuma yana ganin hakan zai fi da ace an kyale ‘yan bindigar suna cin karen su babu babbaka
  • El-Rufai ya ce dakarun Najeriya ba su da kayan aiki, kuma suna bukatar kwarewa a fannin sadarrwa da kuma karin jami’an tsar

Gwamnan Kaduna, Nasir el-Rufai, yace “jami’an tsaro zasu dasa bamabamai a dazuka” domin share barayin daji.

Gwamnan yayi maganar ne a wata tattaunawa da yayi da Arise TV, a ranar Litinin 3 ga watan Janairunn shekarar 2022.

El-Rufai ya danganta rashin iya Kawo karshen barayin dajin da jami’an tsaro keyi a fadin yankin Arewa maso Yamma, da rashin ishasshen kayan aiki, ya kara da cewa

Nasir El-Rufai
Nasir Ahmed El-Rufai

“karin isassun jami’ai, fasahar sadarwa, da kuma kayan aikin tsaro, zai taimaka wajen share yan ta’addan gabaki daya”.

“Yan ta’addan suna aikine a wajen dazukan dake kusa da gari, saboda maboyarsu tana cikin dajin. Babbar matsalace. Hukumomin tsaro suna iya bakin kokarinsu amma an linkasu” Kama yadda ya fada.

“Gaskiya itace, bamu da isassun kayan aiki a kasa da zamu magance matsalolin tsaro da yawa da muke fuskanta, kuma wadannan matsalolin tsaro mabanbantan junane, da suka fantsama a cikin kasa. Babu wani bangare na Najeriya da bashi da wannan matsalar tsaro.

“A karo yawan kayan aiki fasahar sadarwa dakuma bunkasa yawan makamai, a kauda wadannan bata garin gaba daya “.

” Na yarda koda yaushe cewa, zamu dasa bamabamai ne kawai a dazuzzukan, in yaso daga baya ma sake dasa wasu bishiyun. Zamu tashi dazukan gaba daya tare da su dukan su. Za’a samu barna kam, amma a gama dasu, kuma jama’a su dawo gidajensu, su ci gaba da noman su, domin bunkasa tattalin arziki yafi”.

Kamar yadda aka sani dai, Jihar Kaduna tana daga cikin jerin Jihohin dake fuskantar matsalar tsaro, kuma gwamna Nasir Ahmed El-Rufai na daga cikin gwamnonin da keda da tsaurin ra’ayi akan yan ta’addan. Domin shi yana ganin ma bai kamata ayi sulhu da su ba, sulhu daya ne kawai a kashe su.

‘Yan bindiga sun kashe mutum 13, sun yi garkuwa da 46 a Kaduna

‘Yan bindiga sun hallaka mutum sha uku a Kaduna da Taraba, tare da yin garkuwa da mutane 46, inda mutum 18 suka fito daga gida daya.

Yankin da al’amarin ya afku sun hada da unguwar Zalla Udawa da ke karamar hukumar Chikun inda aka kashe mutum daya tare da yin garkuwa da mutane 18 duka ‘yan gida daya.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:30 na safiyar Lahadi a lokacin da ‘yan bindigan suka dira a kauyen da ke kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Dagacin garin Udawa, Muhammed Umaru, shine ya bayyanawa Gidan Jaridar Daily Trust sunan Marigayin mai suna Bala Jaja.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe