27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

‘Yan bindiga sun kashe mutum 13, sun yi garkuwa da 46 a Kaduna

Labarai'Yan bindiga sun kashe mutum 13, sun yi garkuwa da 46 a Kaduna

‘Yan bindiga sun hallaka mutum sha uku a Kaduna da Taraba, tare da yin garkuwa da mutane 46, inda mutum 18 suka fito daga gida daya…

Yankin da al’amarin ya afku sun hada da unguwar Zalla Udawa da ke karamar hukumar Chikun inda aka kashe mutum daya tare da yin garkuwa da mutane 18 duka ‘yan gida daya.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:30 na safiyar Lahadi a lokacin da ‘yan bindigan suka dira a kauyen da ke kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Dagacin garin Udawa, Muhammed Umaru, shine ya bayyanawa Gidan Jaridar Daily Trust sunan Marigayin mai suna Bala Jaja.

Cikin wadanda akayi awon gaba da su akwai matan aure, tsofaffi da kuma ‘yan mata.

“Waɗannan mutane ne da na sani sosai domin kuwa dukanmu matsugunin mu daya. Bala Jaja ya kasance sanannen matashi ne a cikin al’umma wanda aka kashe a lokacin da ya fito don agazawa makwabtan sa da aka yi awon gaba da kimanin mutum 18,” inji shi.

Hakazalika Dagacin ya kara da cewa an kai wani hari makamancin haka a wani kauyen da ake kira da Kerawa da ke cikin karamar hukumar Giwa, inda aka yi garkuwa da wasu daga cikin mutanen yankin kimanin su 16 tare da kashe mutum biyar.

Wani tsohon kansila a yankin, Mai suna Daiyabu Kerawa, wanda ya kara tabbatar wa Gidan Jaridar Daily Trust faruwar lamarin, ya ce garin ya zama kaman kufai a dalilin harin da aka kai.

A cewarsa, an yi jana’izar wadanda lamarin ya shafa da misalin karfe 1 na ranar Lahadi cikin fargaba da tsoro.

“’Yan bindigar sun hallaka mutane biyar tare da sace wasu mutum 16. Yanzun nan ba a jima ba muka kammala jana’izar su. Babban abun bakin cikin shi ne babu wata hukumar tsaro da ta kawo mana dauki a lokacin harin duk da cewa an sanar da su,” inji shi.

Wani mazaunin yankin mai suna Jamilu ya ce mata, manya da kuma kananan yara sun tsere sun bar kauyen saboda tsoron kada ‘yan bindiga su sake kai musu hari.

Ka tuna da alkawuran da ka yiwa ‘yan Arewa kafin ka hau mulki, Dattawan Arewa sun roki Buhari ya dubi yankin

Kungiyar Dattawan Arewa (ACF) sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya mayar da hankali wajen kawo karshen matsalar tsaro a kasar a shekarar 2022, inda suke tunatar da shi akan cewa wannan yana daya daga cikin dalilin da ya sanya mutane suka zabe shi a shekarar 2015.

Kungiyar ta gayawa shugaban kasar da Hafsoshin sojin Najeriya, cewa ‘yan Najeriya suna bukatar kwanciyar hankali da tsaro a duk inda suka shiga a Najeriya daga wannan shekarar.

Sakataren yada labarai na kungiyar, Ammanuel Yawe, wanda ya bayyana haka a wata hira da yayi da jaridar Tribune, ya kuma bukaci gwamnoni da shugabannin kananan hukumomi da su tallafawa gwamnatin tarayya ta hanyar samar da hanyoyin kawo karshen ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’addanci.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe