23 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

A cikin fim na koyi yadda ake garkuwa da mutane – Cewar matashi da ya sace dan shekara 6

LabaraiA cikin fim na koyi yadda ake garkuwa da mutane - Cewar matashi da ya sace dan shekara 6

Wani matashin saurayi da rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama da laifin sace wani yaro dan shekara 6, ya bayyana cewa ya koyi yadda ake garkuwa da mutane a wajen jarumin Nollywood Zubby Michael, wanda yake yawan fitowa a matsayin mai garkuwa da mutane a cikin fim.

Saurayin da aka bayyana sunan shi da Ayobamidele Kudus Ayodele ya sace yaron a makarantar su dake Ojo, cikin yankin Alaba dake jihar Lagos, a ranar 16 ga watan Nuwambar shekarar 2021.

Bayan sace yaron Kudus ya ajiye yaron na tsawon kwana hudu a hannun shi har zuwa lokacin da aka biya shi sama da dubu dari biyar a matsayin kudin fansa kafin ya saki yaron.

Jarumin fim Zubby Michael
Jarumin fim Zubby Michael

A rahoton da jaridar Vanguard ta fitar, matashin ya bayyana cewa:

“Zubby Micheal shine jarumin dana fi so a Nollywood, kuma ya iya fitowa a matsayin mai garkuwa da mutane a fim. Na yanke shawarar amfani da irin salon da Zubby yake amfani dashi wajen sace yara da manya a fim.

“Na fara da ziyartar makarantu da dama a yankin Ojo domin na samu hanyar daukar yara ba tare da kowa ya gani ba. A ranar 16 ga watan Nuwambar shekarar 2021, na ziyarci wata makaranta a kusa da kasuwar Alaba na tsaya a bakin kofar makarantar.

“Na ga wasu yara suna zuwa makaranta daya da bulala a hannun shi, sai na tsayar da su na ja su da hira, na karbi bulalar nake tambayar shi a ina ya saya, sai yake gaya mini sunan wajen, sai na tambayeshi ya raka ni wajen. Na rada masa a kunne cewa zan siya masa Chocolate da Biskit.

“Saboda gudun kada wani ya ganni, sai na dauki yaron zuwa wani otel a Ilogbo Eremi, cikin birnin Lagos. Na kira mahaifin yaron na bukaci ya biya Naira Miliyan biyu (N2m). Mun shafe kwanaki hudu a wajen kafin iyayen shi su samu su hada N550,000. Yaron bai da mu ba a lokacin da muke cikin otel din, saboda na bashi waya ta wacce ke cike da games kala-kala.

“Ina nadamar halin da na sanya iyayen shi a ciki. Ni ba dan kungiyar asiri bane, kuma ni ba dan fashi da makami bane. Bani da wata kungiya. Kawai na gwada kwarewa ta ne ta hanyar kallon fim din Zubby Micheal. Iyaye na sun bani tarbiya yadda ya kamata, kawai dai rashin hakuri ne da son abin duniya ya rude ni.”

Matsalar garkuwa da mutane don neman kudin fansa na cigaba da ciwa al’ummar Najeriya tuwo a kwarya.

Hukumomin tsaro na iya bakin kokarin su wajen ganin sun kawo karshen lamarin, amma abin ya ci tura, inda matsalar tafi kamari a yankunan jihohin Sokoto, Zamfara, Katsina, Niger, Kaduna da sauran su.

An kama matar aure da take soyayya da mai garkuwa da mutane

A cigaba da yaki da ake da masu garkuwa da mutanen hukumar ‘yan sanda ta jihar Kaduna ta kama wata mata mai suna Mariya Abubakar mai shekaru 35 a duniya da take soyayya da wani mai garkuwa da mutane duk kuwa da kasancewar ta matar aure.

A wata hira da Mariya ta yi da hukumar ‘yan sandan jihar ta Kaduna wadda ROOTS TV ta nada, ta bayyana cewa har daji take zuwa ta samu saurayin nata su sheke ayar su kana ta kai musu wasu matan don debe musu kewa da kuma biyan bukatun su.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe