34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Masari ya bukaci a kyale ‘yan Kudu suyi shugabanci bayan Buhari ya kammala mulki a 2023

LabaraiMasari ya bukaci a kyale 'yan Kudu suyi shugabanci bayan Buhari ya kammala mulki a 2023

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya sake bayyana matsayar shi kan mika mulki ga Kudancin Najeriya, inda yace hakan zai taimaka sosai wajen canja tsarin yadda Najeriya take a yanzu.

Masari ya bayyana hakane a lokacin da yake hira da manema labarai a gidan shi ranar Talata 28 ga watan Disambar 2021.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, gwamnan ya ce:

“Bari na bayyana matsaya ta kuru-kuru. Wannan kundin tsarin mulki na kasa mu muka rubuta shi, ba wai shine ya rubuta mu ba. Kwarai kundin tsarin mulki bai ce mu mika mulki kudu ba, amma idan kun mika mulkin kun saba doka ne?

“A gani na, kuma a matsayina na Aminu Bello Masari, har sai lokacin da muka zama masu gaskiya, ina ganin mulkin karba-karba zai taimaka wajen kawo gyara ga tsarin mu. Ina goyon baya kuma har yanzu ina nan kan matsaya ta, kuma ina da damar da zanyi wannan magana,” a cewar shi.

Masari ya ce shi mamba ne na taron da aka yi na kundin tsarin mulki a shekarar 1994/1995, a lokacin da aka fito da hukumar “Federal Character Commission”, ya kara da cewa yana kuma daga cikin ‘yan kungiyar a shekarar 1999, kuma kwamitin su ta bukaci kowanne yanki a basu damar yin mulki na tsawon shekara biyar, amma wannan matsaya da suka tattauna a kai bata cimma gaci ba.

Haka kuma Masari ya yi kira ga ‘yan siyasa, ‘yan jarida, shugabannin addini dana gargajiya da su dinga sanya Najeriya farko a dukkan abinda za su yi a yayin da zaben shekarar 2023 ke tinkarowa.

“Muna ganin siyasa a matsayin wata hanya ta kawo shugabanci nagari. Sai dai kuma har yanzu siyasar mu bata da tsafta, tun daga lokacin samun ‘yancin kai zuwa yanzu, muna maganar shekara 60 kenan, inda hakan na da matukar muhimmanci a rayuwar mutane, ammaa kuma ga kasa baki daya, wannan aikine mai gudana.”

“Mu dinga duba ga inda muke a baya, da kuma inda muke a yau da kuma inda zamu je a gobe. Matsalar ita ce muna da gaggawar da tun kafin mu gama rarrafe muna son mu fara gudu,” ya ce.

Masari ya ce ‘yan siyasa ya kamata su canja halayensu, saboda suna bukatar daukar nauyin dake kansu na shugabanci da kuma duk wahalhalun dake cikin fitowa takara.

“Na tabbata ‘yan jarida su ma suna da tasu gudummawar da ya kamata su taka. Misali a yanzu da muke tinkarar 2023, wajen da kafafen sadarwa suka fi bawa muhimmanci shine albashin ‘yan majalisu, ba wai akan abinda ‘yan majalisun suke yi ba da kuma abinda ya kamata su yi ba. Saboda haka kafafen sadarwa ta kirkiri wata hanya da kowanne mutum yake son zuwa saboda kudin dake wurin ba wai aikin da zai yi ba.”

Mutanen Borno su kyale Zulum ya cigaba da yi musu gwamna har illa Masha Allah – El-Rufai

Bayan kaddamar da ayyukan da gwamnatin jihar Borno tayi, gwamnan Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi kira ga mutanen jihar Borno akan kara zaben Babagana Zulum a karo na biyu, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Ya yi wannan kiran ne a ranar Alhamis a Maiduguri yayin da ya halarci taron kaddamar da wasu ayyukan gwamnatin jihar wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi.

Gwamnan ya nuna jin dadinsa akan yadda abubuwa su ka gyaru a cikin Maiduguri. Kamar yadda yace, “Ina matukar farin ciki. Wannan ne karona na farko a Maiduguri tun bayan Kashim Shettima na gwamnan jihar kuma an samu gyara kwarai akan tsaro da tattalin arzikin jihar wanda hakan ya faranta min rai.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe