34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Manyan dalilai guda 3 da ya sanya kotu taki yiwa Maryam Sanda afuwa

LabaraiManyan dalilai guda 3 da ya sanya kotu taki yiwa Maryam Sanda afuwa
  • Bayan yanke mata hukuncin kisa da kotu tayi a Abuja a watan Janairun shekarar 2020
  • Maryama ta garzaya zuwa ga kotun daukaka kara domin nemawa kanta adalci, inda a cewarta Alkalin da ya yanke mata hukunci bai yi mata adalci ba
  • Sai dai kuma kash, a wannan karon ma dai hakar ta bata cimma ruwa ba, domin kuwa kotun daukaka karar tayi watsi da wannan kara da ta shigar

A yunkuri na farko da Maryam Sanda tayi na mika kokenta ga babbar kotu kan hukuncin kisa da aka yanke mata, a ranar Juma’a 4 ga watan Disamba, bata cimma nasara ba, inda hakan ya dawo da kace-nace da aka yi tayi a baya a wannan lokaci.

Kotun wacce mai shari’a Stephen Adah ke jagoranta tayi watsi da korafin da Maryam Sanda ta shigar gabanta a ranar Juma’ar nan da ta gabata.

Idan ba a manta ba dai, an kama Maryam Sanda da laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello, wanda yake dan uwane ga tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa.

KU KARANTA: Rikita-rikita: APC ta lashe zaben kujerar Sanata a jihar Imo ba tare da dan takara ba

A ranar 27 ga watan Janairun shekarar 2020 dinnan ne dai wata babbar kotu dake zaune a Abuja ta yankewa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan ‘yan sanda sun kamata da laifin kisan a watan Nuwambar shekarar 2017.

Da yake gabatar da shari’ar, mai shari’a Yusuf Halilu yace akwai kwararan shaidu da ya sanya aka yi watsi da batun Sanda na cewa mijinta ya fadi akan tukunyar Shisha da ta fashe ne a lokacin da suke fada inda hakan yayi sanadiyyar mutuwarsa.

A yayin da wannan shari’a ta sake tada kura, jaridar Legit.ng ta kawo dalilai guda uku da ya sanya hukuncin da mai shari’a Yusuf Halilu ya yankewa Maryam Sanda aka yi watsi dashi a kotun daukaka kara.

  1. Rashin kwararan dalilai

Maryam Sanda ta tinkari kotun daukaka karar inda ta roke ta akan tayi watsi da hukuncin da kotun baya ta yanke mata, inda tace kotun bata yi mata adalci ba kan hukuncin kisan da ta yanke mata.

A rokon da Maryam ta yiwa kotun daukaka karar, ta ce alkalin kotun yayi son kai wajen yanke mata hukunci, inda tayi zargin cewa Mai Shari’a Yusuf Halliru, ya yanke hukunci akanta duk da shakkun dake tattare da shaidun.

“An yanke hukuncin ne ta hanyar shaidar da shaidu suka bayar, ba’a samu makamin da aka yi kisa dashi ba, rashin shaidu da suka kai mutum biyu ko sama da haka, da kuma rashin rahoto na binciken asibiti dake nuna shaidar ainahin abinda ya kashe mijinta.”

Amma a shari’ar da aka yi ta tsawon awanni biyu, kwamitin kotun tayi watsi da wannan kara da Maryam ta shigar, saboda rashin cancanta.

2. Hukunci bisa yadda doka ta tanada

Da take yanke hukunci a ranar Juma’a, Alkalin kotun Stephen Adah, ta ce babu wani dalili da zai sanya ayi watsi da hukuncin da kotun baya ta yanke.

Haka kuma kotun tace bayan rashin cancanta akan daukaka kara da Maryam Sanda tayi, shaidun da ta gabatar basu da wata ma’ana, saboda haka dole a yanke hukunci bisa yadda doka ta tanada.

KU KARANTA: Fatima Isa: Direbar jirgin kasa ta farko da aka dinga yiwa dariya lokacin da ta fara aiki yanzu ta zama abin sha’awa

3. Kasa tabbatarwa da kotu cewa Bello ya fada akan kwalbar Shisha lokacin da suke fada

Daya daga cikin shaidun da Sanda ta mikawa kotun daukaka kara, tace mijinta Bello, ya fadi akan kwalbar Shisha ne a lokacin da suke rikici.

Amma kuma kotun tayi watsi da wannan magana, Alkalin kotun Stephen Adah, ta ce wannan shaida da ta bayyana bata isa ta sanya kotun ta yadda cewa kisan tayi ba tare da niyya ba.

Zamu garzaya zuwa Kotun Koli – Cewar Lauyan Maryam Sanda

Wani babban lauya a Najeriya wanda ke jagorantar daukacin lauyoyin dake kare Maryam Sanda, ya bayyana cewa tabbas akwai lauje cikin nadi akan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke akan Maryam Sanda.

Da yake yiwa manema labarai jawabi bayan yanke hukuncin da kotu tayi, yace Maryam za ta garzaya zuwa kotun koli domin nemawa kanta adalci.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/laabarunhausa/

Twitterhttps://www.twitter.com/labarunhausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: labarunhausaa@gmail.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe