23 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

An yaudari ‘yan Najeriya, tarin kwali babu sana’ar hannu babbar matsala ne, Injiniya Mustapha Habu

LabaraiAn yaudari ‘yan Najeriya, tarin kwali babu sana’ar hannu babbar matsala ne, Injiniya Mustapha Habu

Najeriya – Gidan talabijin din Tambarin Hausa sun tattauna da Injiniya Mustapha Habu kamar yadda Engausa Global Hub su ka wallafa a shafin su na Facebook inda ya dinga bayanai akan amfanin sana’ar hannu baya ga ilimin boko ga ‘yan Najeriya.
Injiniya Mustapha Habu wanda shi ne CEO kuma wanda ya samar da ENGAUSA GLOBAL TECH HUB sannan kuma kwararre ne wurin koyar da matasa akan ilimin fasaha iri-iri na gyare-gyaren wayoyi, harkar CCTV Camera, samar da wuta ta hasken rana da kuma harkokin yanar gizo wanda mutum zai iya dogaro da kansa.

An yaudari ‘yan Najeriya, tarin kwali babu sana’ar hannu babbar matsala ne, Injiniya Mustapha Habu


A cewarsa, kasashen da su ka ci gaba kamar China suna tallafa wa masu kananun sana’o’i don su samu abin dagora da kawanansu sannan gwamnatin ta amfana ta harajin da za ta kallafa wa kamfanonin.
Kamar yadda injiniyan ya ce yayin tattaunawar wacce yace sun yi hira da wani inda yake ce masa:

“Ka ga matsalar ku ta ‘yan Najeriya, an yaudareku da tara kwalaye. Kai yanzu babu kwalin da kake bukata, shago ya kamata ka bude.”


Ya bayyana muhimmancin bude wurin sana’a inda yace zaka iya daukar wani aiki ba tare da ka jira gwamnati ba.
Ya ce akwai manyan injiniyoyi da suke wucewa kasar China inda suke bude shaguna don dogaro da kawunansu, kuma su na koyon ilimin fasaha iri-iri wanda hakan zai taimaka wurin rage rashin ayyukan yi a kasa ta hanyar hana matasa barace-barace da maula a cikin gari.
Injiniyan ya bayyana yadda bincikensa ya nuna masa cewa kasashe irin su China su ke samun kudade ta kamfanoni masu tasowa.

Matukar ana so a yi nasara, Dole sai sojoji sun zakulo ‘Yan ta’adda har Maboyarsu, Gwamna Zulum

Kungiyar gwamnonin arewa maso gabas sun shirya taro na shida kenan sakamakon yadda matsalar tsaro a arewa maso yammacin kasar nan a kullum ke kara tabarbarewa.
Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya yi kira ga rundunonin sojin Najeriya inda ya bukaci su kara jajircewa wurin bin maboyin ‘yan ta’addan da ke dazuka don yakar su.

Kamar yadda gwamnan ya shaida, wannan ce kadai mafitar da za ta kawo karshen farmakin da ‘yan Boko Haram da sauran ‘yan ta’addan su ke kai wa arewacin Najeriya.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe