22.1 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Waka halas ce, Annabi (SAW) ma ya saurara, Sheikh Ibrahim Khalil Kano

LabaraiWaka halas ce, Annabi (SAW) ma ya saurara, Sheikh Ibrahim Khalil Kano

Waka – Fitaccen malamin nan na jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil ya yi fashin baki akan wakoki wanda wasu malamai su ke kallo kai tsaye suce haramun ne yi da sauraron su.
Kamar yadda malamin ya ce a wata hira da BBC Hausa ta yi da shi, akwai halastattu da kuma haramtattun wakoki.
Malamin ya ce matukar waka babu batsa cikinta ko kuma zagi ko suka, halas ne yinta da sauraronta.

Khaliil
Waka halas ce, Annabi (SAW) ma ya saurara, Sheikh Ibrahim Khalil Kano


Amma wakokin da zasu siffanta mace ko kuma namiji har mutum ya ji sha’awa a jikinsa ko kuma yabon caca ko giya ba su da kyau a yi ko a sauraresu.
Malamin ya kafa hujja akan cewa akwai ranar da Annabi Muhammad SAW ya taba sa wani ya yi masa waka har sai da ya yi baitoci dari na wakar wani mutum wanda ba musulmi bane asalin mawakin.
A cewarsa, har dakatawa ya yi amma ma’aikin Allah ya bukaci ya ci gaba da yin wakar.
Ya kara da bayar da hujjoji gamsassu inda ya ce akwai fa’idoji da dama na waka kamar samar da nishadi, kwanciyar hankali, rage gajiya, samar da fikira da basira, fadakarwa da sauransu.
Ya ce har Sayyidan Aliyu ma yana sa wa a yi masa waka wajen majalisi don a samu nishadi sannan nassi na Al’Qur’ani na suratul Yaseen da suratul Shu’ara’i sun tantance akan waka mai kyau da waka mara kyau.

Wani mawaki ya rangada wa shugaban ‘yan bindiga, Bello Turji, hadaddiyar waka ya na jinjina masa

Wani mawaki ya gwangwaje fitaccen dan bindiga, Bello Turji, wanda ya addabin jihohin Zamfara, Sokoto da wasu sassan Nijar da wakar yabo.

Wata waka da aka yi ta da harshen Hausa wacce ta kai tsawon minti 14 ta bazu cikin gari inda aka ji wani mutum wanda ya kira kansa da Adamu Ayuba tare da wata mace su na kambama shugaban ‘yan Bindiga, Bello Turji cike da yaba wa jarumtarsa.
Wakar ta nuna tsantsar yabo ga Turji wacce yanzu haka ta fara yawa a arewacin Najeriya inda mutane da dama su ke shan kashi a hannun rikakken dan bindigan.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe