27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Jaruma Aisha Najamu ta Izzarso ta yi bidiyo tana rusa kuka saboda masu zaginta akan rawar TikTok

LabaraiKannywoodJaruma Aisha Najamu ta Izzarso ta yi bidiyo tana rusa kuka saboda masu zaginta akan rawar TikTok

Sabuwar jaruma Aisha Najamu wacce ta samu shahara bayan bayyanarta a shirin fim din Izzar so ta yi bidiyo tana rusa kuka akan wadanda su ke ce mata karuwa idan tana raye-rayenta na TikTok.
Aisha Najamu ta bukaci masu zaginta da su kasance masu tsoron Allah don TikTok wajen nishadi da debe kewa ne, amma abinda ya ke bata takaici shine yadda mutane suke tsokaci mara kyau a karkashin bidiyoyinta.

AIsha Najamu
Jaruma Aisha Najamu ta Izzarso ta yi bidiyo tana rusa kuka saboda masu zaginta akan rawar TikTok


Jarumar ta fara da cewa da farko ba mutum bai sa musu data ba sannan basu matsa wa kowa ya kalli bidiyonsu ba amma a dinga kiransu da karuwai.
Aisha Najamu ta kara da jan kunnen jama’a inda tace kowa yana da ‘yan uwa, kanni, mata da iyaye amma ya ke jifar wasu da kalmar karuwanci.
A cewarta duk wata kalma da mutum ya furta sai ya tsaya gaban Allah ranar tashin Alkiyama don tabbatar da furucinsa.
Allah yasa masu yi su ji kuma su gane gaskiya.

Duk namijin da ya ke barin matarsa ta na rawar TikTok ba zai ji kamshin Aljannah ba, Jaruma Rukayya Dawayya

Jaruma Rukayya Dawayya a wani bidiyo da ta yi wanda Hadiza Gabon ta wallafa a shafinta na Facebook ta ja hankali ga mata musamman masu aure da su ke raye-raye a shafukansu na TikTok.
Jarumar ta fara ne da bayar da wani labari takaitacce wanda ta ce ya auku da ita a lokacin tana da aure.
Jarumar ta fara da bayyana yadda wasu shakikan kawayenta su ka kai mata ziyara gidanta da ke Abuja bayan ta ci kwalliya amma mijinta bai gani ba.

Tun samun labarin sun kai mata ziyarar our ta nuna a sanar dasu cewa bata nan duk don kada su ga kwalliyarta kafin mijinta.
A cewar jarumar, har sai da mijinta ya dawo ya ga kwalliyar sannan daga bisani ta kira su ta ce musu ta dawo daga inda ta je.
Daga karshen bidiyon ta ce duk macen da ke yin kwalliya ta wallafa bidiyon kwalliyar a TikTok bata son mijinta, yayin da mazan da su ke barin matansu su na bidiyon ba sa kaunar matan kuma basa kishinsu.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe