22.1 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Yadda Budurwa ta tsinka wa saurayinta mari a kasuwa saboda kin amincewa da tayin aurenta

LabaraiYadda Budurwa ta tsinka wa saurayinta mari a kasuwa saboda kin amincewa da tayin aurenta

Bidiyon yadda wata budurwa ta gaura wa saurayinta mari gaban jama’a akan kin amincewa da tayin aurenta ya janyo cece-kuce.
Bidiyon ya dauki hankali bayan an ga yadda budurwar ta durkusa har kasa tana yi wa saurayin tayin aurenta a wurin siyayya amma ya murje idanu ya ki amincewa.

Budurwa da saurayi
Yadda Budurwa ta tsinka wa saurayinta mari a kasuwa saboda kin amincewa da tayin aurenta


Ganin ta dade a kasa sai yayi kokarin amfani da hannunsa don ya dago ta ta mike tsaye.
Hankulan mutane da dama da ke wurin ya koma kansu bayan ganin yadda saurayin ya tsinka ta hanyar kin amincewa da tayinta ta daga hannu ta sharara masa mari.
Bidiyon wanda Foreverdope ta wallafa a YouTube ya nuna yadda budurwar ta yi borin kunya ta hanayar gaura masa mari.
An samu bayanai akan yadda su ka kwashe shekaru 6 su na soyayya.

Matata ta tsinka min mari ina tsaka da fallasa yadda take tara fitsari a uwar-daka a gidan rediyo

Wata mata ‘yar kasar Ghana ta nuna fushinta lokacin da ta dauke mijinta da mari bayan ya bayyana yadda ta ke tara fitsari a gaban dan jaridan m gidan rediyon Nhyira FM.
Gidan rediyon a yankin Ashanti yake a cikin kasar Ghana.

Ta ci zarafin mijinta a gaban dan jaridar, mai gidansu da sauran bakin da aka gayyata don tattaunawa da su.
Ya fallasa yadda ta ke ajiye fitsari mai yawa a uwar dakansu duk da su na da bayi.
Mutumin ya kara da bayyana yadda matarsa ba ta wanke sutturun yaransu. Kamar yadda ya ce, ta gwammaci ta tsula fitsarinta a daki kuma ta ajiye a dakin, kafin ya kammala magana ta gaura masa mari.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe