24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Rikita-rikita: APC ta lashe zaben kujerar Sanata a jihar Imo ba tare da dan takara ba

LabaraiRikita-rikita: APC ta lashe zaben kujerar Sanata a jihar Imo ba tare da dan takara ba
  • Bayan gabatar da zaben sanata a jihar Imo da aka gabatar a jiya Asabar a jihar
  • Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta bayyana jam’iyyar APC a matsayin jam’iyyar da ta lashe zaben kujerar sanatan
  • Sai dai wani abin mamaki har yanzu hukumar ba ta gabatar da dan takara koda guda daya ba daga jam’iyyar a matsayin wanda ya lashe zaben

Duk da dai cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, a ranar Lahadi, 6 ga watan Disamba ta bayyana cewa babbar jam’iyyar APC mai mulki ce ta lashe zaben kujerar Sanata a jihar Imo ta Arewa, har ya zuwa yanzu dai ba ta bayyana dan takarar da ya lashe zaben ba.

A yanzu haka dai da Ifeanyi Araraume da kuma Frank Ebizim, suna kalubalantar tikitin takarar na jam’iyyar APC, inda hakan yayi sanadiyyar tada kararraki da yawa a kotu.

KU KARANTA: Fatima Isa: Direbar jirgin kasa ta farko da aka dinga yiwa dariya lokacin da ta fara aiki yanzu ta zama abin sha’awa

Kamar dai yadda jam’in hukumar INEC, Hakeem Adikum, ya bayyana, jam’iyyar APC ta lashe zaben kujerar Sanatan da kuri’a 36,811, yayin da dan takarar jam’iyyar PDP, Emmanuel Okewulonu ya zo na biyu da kuri’a 31, 903, kamar dai yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Adikum ya kara da cewa APC ta lashe kananan hukumomi guda biyar a cikin guda shida dake wannan yanki, inda ita kuma jam’iyyar PDP ta lashe karamar hukuma guda daya kacal.

Ya ce:

KU KARANTA: Hotunan kafin aure na dan gidan El-Rufai ya jawo hankalin mutane da dama a shafukan sadarwa

“Ina gabatar muku da jam’iyyar All Prrogressive Congress, a matsayin wacce ta lashe zaben kujerar Sanata da aka gabatar a jihar Imo ta Arewa a ranar Asabar, 5 ga watan Disamba.”

Jami’in hukumar zaben ta kasa ya bayyana cewa hukumar ta kasa warewa tsakanin Araraume da Ibezim a matsayin wadanda suka lashe takarar, saboda takunkumin da kotu ta sanya a kansu.

Idan ba a manta ba a watan da ya gabata ne aka gabatar da zaben shugaban kasa a kasar Amurka, inda yanayin yadda zaben kasar ya gabata ya jawo kace, nace matuka a kafafen sadarwa.

Amurka dai ana yi mata kallo a matsayin kasa abar koyi a fannin dimokuradiyya, amma yadda zaben ya wakana a kasar ya sanya mutane sun fara wasu-wasi akan sahihancin dimokuradiyyar kasar.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/laabarunhausa/

Twitterhttps://www.twitter.com/labarunhausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: labarunhausaa@gmail.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe