27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Wallafar Nazir Sarkin Waka a Instagram yana goyon bayan dukan mata ya tayar da kura

LabaraiKannywoodWallafar Nazir Sarkin Waka a Instagram yana goyon bayan dukan mata ya tayar da kura

Babban mawaki Nazir Sarkin waka kuma jarumin fina-finai lya janyo cece-kuce sakamakon wata wallafa da yayi a shafinsa na Instagram.
A shafinsa mai suna Sarkin_Wakar_San_Kano ya sha zagi da caccaka daga mutane da dama musamman mata wadanda su ka yi ta alawadai akan wannan fahimtar tashi.

Naziru Sarkin waka
Wallafar Nazir Sarkin Waka a Instagram yana goyon bayan dukan mata ya tayar da kura


A ranar Litinin da yamma ne sarkin waka ya dauki hoton wani fallen daga cikin Al’Qur’an mai girma inda ya ke nuna da ayar da ta yi magana akan dukan mata. A karkashin hoton yace:

“Toh, ni dai naga ayar da tace mutum ya daki matarsa idan taci tura… Sai dai a taya ni nemo wacce take kar a daki mata…nagode.”

Wannan wallafar ta sa ta sa mutane da dama sun yi ta sukarsa Sarkin waka wasu na cewa alama ce da ke nuna yana dukan nashi matan.
Akwai wadanda su ka dinga cewa mutuncinsa ya zube a idanunsa saboda da alamun bai san tafsirin ayar da kyau ba.
A ranar Talata kuma ya kara yin wani dogon bidiyo wanda yace haka ayar take kuma yana nan a kan bakarsa.
Ya kara da cewa yana da matar da suka kwashe shekaru 8 ba tare da wani ya sasanta tsakaninsu ba saboda zaman lafiya.
Ya kara da jaddada batun dukan mata matsawar ba ba ta jin magana. A cewarsa haka ayar tazo kuma haka fassararta take.
Daga karshe ya hori maza da su guji dukan matansu sannan mata su kasance masu bin dokokin mazajensu.

Ga kadan daga cikin tsokacin jama’a:

teemash_food_and_catering ta ce:

“To tunda kace sai kayi addu’a a fara da yaranka in sunyi ba dadi. Mudai iyayen ‘yan mata mu na neman tsari da mijin da zai dake mu ko ya daki yaran mu.”

adamu_dan_borno ya ce:

“Malam ka tsaya a iya baran kah…wannan bangaren ba naka bane.”

Janbulo19 ya yi tsokaci da:

“Ranka ya dade wannan ba girmanka bane.”

Batun zubar da cikin Rahama Sadau, daga ina batun ya samo asali?

Labarin zubar da cikin jaruma Rahama Sadau, daga ina batun ya ke ne?

Wani mai jan hankali a dandalin TikTok kamar yadda Tashar Tsakar Gida ta ruwaito, ya tura budaddiyar wasika ga Sheikh Isa Ali Fantami akan batun rufe TikTok, anan ya kara da yin wata magana dangane da Rahama Sadau da nufin a yi mata nasiha a kan wani abu da yake kokwanton kasancewarsa.

Amma ya ce ya kamata ko da gaskiya bane ya kamata a ja mata kunne.
Abinda malamin ke son a yi mata nasiha ko kuma yake zargin ance ta wallafa a kafar sada zumunta shine yadda a wata hira da aka yi da ita tace ita budurwa ce amma ba dal a leda ba kuma ta zubar da ciki sau da dama amma wai ba za ta iya boye hallayarta ta banza ba don hakan munafinci ne.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe