23 C
Abuja
Sunday, September 25, 2022

Nan da shekaru 7 za a hura kaho, cewar Baturen da ya ci gaba da rayuwa a kangon gini

LabaraiNan da shekaru 7 za a hura kaho, cewar Baturen da ya ci gaba da rayuwa a kangon gini

Wani Baturen Amurka ya ci gaba da zama a wani tsohon kangon gini kuma ya ce ba ya da niyyar kwashe kayansa don tashi daga gidan ko kuma gyara ginin.


Leslie Southam ya yarda da cewa nan da shekaru 7 za a hura kaho don duniya na gab da tashi.

Duniya
Nan da shekaru 7 za a hura kaho, cewar Baturen da ya ci gaba da rayuwa a kangon gini


Yayin da wasu suke aure, wasu kuma su ke ta neman kudi, Leslie mai shekaru 53 a duniya ya ce babu wani dan Adam da zai ci gaba da wanzuwa a bayan kasa nan da shekaru 7 masu zuwa.


Ya ce ko gyara gidansu ba zai yi ba, yana zaune ya na jiran lokacin hura kaho ya yi.
Ya ci gaba da zama a kangon beneda ke Brynmefys Wale a Amurka tare da tsofaffin iyayensa.


Tun shekarar 1980 aka siya gidan da suke zaune, har yau ba su taba gyara ginin ba.
Ya sanar da dalilinsa na yarda da cewa nan da shekaru 7 duniyar za ta kare a wata tattaunawa da Wales Online su ka yi da shi, inda ya ce ko cutar COVID-19 ma alamar tashin duniya ce.


Ya kwatanta lalacewa saman kwanon gidaje, tara bololi da lalacewa motocin a matsayin alamar karshen duniya inda yace kasa ce take son hadiye komai.


A cewarsa alamu sun nuna cewa Jesus ya kusa bayyana, don haka ba za a wuce shekaru 7 ba duniyar zata zo karshe.

Soshiyal midiya ta kusa fashewa bayan bayyanar hotunan uwargidan Gbajabiamila sanye da sutturun N8m

Soshiyan midiya ta dauki zafi bayan bayyanar hotunan Uwargidan kakakin majalisar dattawa, Femi Gbajabiamila sanye da wasu sutturu masu tsadar gaske.


A haotunan matar wacce ta ci kurus rike da wata jaka mai kama ta taliya ‘yar hausa a sukwane ta shayar da mutane mamaki bayan masana gayu sun tabbatar da sutturun da ke jikinta sun kai kimar naira miliyan takwas.

Shafin Infonaija na Instagram ya bayyana hotunan da kudaden sutturar da ta sanya inda aka gano jakar hannunta ta kai kimar $2,661, wanda ya yi daidai da N1,463,550.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe