35.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Tijjani Asase: – Da sana’ar gwangwan da aikin karen mota na fara neman kudi

LabaraiKannywoodTijjani Asase: - Da sana'ar gwangwan da aikin karen mota na fara neman kudi

Tijjani Asase ya bayyana yadda ya fara rayuwa da kuma yadda ya fara neman kudi, inda ya ce da sana’ar gwangwan ya fara neman kudi kafin daga baya ya shiga harkar fim.

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa na masana’antar Kannywood, wanda yake daya daga cikin masu shirya fim dinnan mai dogon zango mai suna “A Duniya”, Tijjani Asase, ya bayyana cewa ya fara neman kudi ne ta hanyar sana’ar gwangwan.

Tijjani Asase, ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da gidan Radio Freedom, inda ya ce bayan sana’ar gwangwan ya kuma yi aikin karen mota, kafin daga baya ya tsunduma cikin masana’antar ta Kannywood.

Asase ya ce:

“Babban abinda yake bani sha’awa a rayuwa shine na ga matashi ya rike sana’ar da yake yi hannu biyu-biyu duk kankantar ta, haka kuma mutum ya rike gaskiya da rikon amana a duk abinda zai yi a rayuwa.

Tijjani Asase
Jarumi Tijjani Asase – Photo: Instagram

Tijjani Asase wanda ya yi kaurin suna a cikin fina-finai wajen fitowa a matsayin dan daba ko kuma wani babban mai laifi, ya yi kaurin suna a cikin fim din shi mai dogon zango na “A Duniya”, inda ya ce ya shafe kusan shekara ashirin a masana’antar ta Kannywood, kamar yadda ya bayyana a wata hira da ya yi da BBC Hausa, a cikin shirin su na “Daga Bakin Mai Ita”.

Jarumin ya yi tsokaci dangane da yadda matasa ke shiga ayyukan laifuka na kwacen waya da sace-sace, inda ya ce:

“Babban abinda yake haifar da kwacen waya a wannan lokaci, shine rashin aikin yi ko dogaro da kai da matasa ke yi, sai kuma suna yiwa masu kananan sana’o’i kallon banza.” A cewar Tijjani Asase.

A karshe jarumin ya yi fatan masana’antar ta Kannywood ta cigaba da samar da fina-finai da su taimaka wajen sauya rayuwar al’umma baki daya.

An maka jaruma Hafsat Idris gaban kotu kan cinye wasu makudan kudade da ta yi

Wani rahoto da gidan Radio Dala FM dake Kano ya kawo a jiya ya bayyana cewa wani kamfani ya kai karar jarumar Kannywood Hafsat Idris, zuwa gaban babbar kotun jahar Kano, wacce ke Ungoggo, kan zargin cinye zunzurutun kudi har naira miliyan daya da dubu dari uku da aka bata domin daukar bidiyon rawa, amma ta saba alkawari.

Rahoton ya bayyana cewa jarumar ta zo gurin bikin, har an fara daukar bidiyon, sai kumaa ta gudu ba ta dawo ba, inda hakan yasa kamfanin ke bukatar kotu ta sa ta dawo musu da kudin su, kana ta biya su naira miliyan goma.

Sun bukaci wannan naira miliyan goma ne a matsayin diiyyar asarar da ta sa suka yi domin, sun tara ma’aikata sun dauko hayar kayan aiki, sai kuma rashin cika alkawarinta yasa sun yi asara.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Dala FM Kano

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe