34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Fatima Isa: Direbar jirgin kasa ta farko da aka dinga yiwa dariya lokacin da ta fara aiki yanzu ta zama abar sha’awa

LabaraiFatima Isa: Direbar jirgin kasa ta farko da aka dinga yiwa dariya lokacin da ta fara aiki yanzu ta zama abar sha'awa
  • Mace ta farko da ta fara tukin jirgin kasa a Najeriya, Fatima Isa Abiola, tayi kira ga mata da su shiga harkar tukin jirgin kasa
  • Ta ce ta fara sha’awar tukin jirgin kasa tun tana shekara 12 a duniya
  • Fatima ta ce mutane sun dinga yi mata dariya a wancan lokacin data fara tukin jirgi, ciki kuwa harda abokanan aikinta maza
  • Ta ce yanzu shekarunta hudu kenan tana tukin jirgin kasa, inda hakan ya kara tabbatar mata da cewa duk abinda namiji zai yi mace za ta iya yin fiya da shi

Mace ta farko da ta fara tuka jirgin kasa a Najeriya, Fatima Isa Abiola, ta bayyana irin abubuwan da ta sha fama da su a lokacin da ta fara wannan aiki.

A wata hira da tayi da BBC, ta ce mutane sun dinga yi mata dariya a lokacin da ta fara wannan aiki, ciki kuwa hadda abokanan aikinta maza.

KU KARANTA: Hotunan kafin aure na dan gidan El-Rufai ya jawo hankalin mutane da dama a shafukan sadarwa

Fatima tana da shekara 12 a duniya ta fara sha’awar tukin jirgin kasa. A cewarta, tana tafiya da kakanta kawai sai suka ga jirgin kasa na zuwa a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, tun a wannan lokacin ta yiwa kanta alkawarin sai ta tuka shi watarana.

Ta ce mutane sunyi tunanin za ta daina aikin bayan shekara daya, amma yanzu haka shekararta hudu tana wannan aiki.

Fatima Isah
Fatima Isah

Fatima ta ce ana bukatar mata su shiga wannan harka ta tukin jirgin kasa, saboda a yanzu haka akwai cigaba da dama da ake samu a wannan harkar.

Fatima tana da burin zama macen da tafi kowa iya tukin jirgin kasa a duniya, sannan kuma ta koyawa mata 100 yadda ake tukin jirgin kasa.

KU KARANTA: Na hannun daman Ganduje ya rabawa matasan yankinsa jakuna domin su dogara da kansu

Yadda hazikin dalibi daga jihar Kano ya samu jinjinar kambun zinare a kasar Indiya

Wani dalibi daga jihar Kano mai karatu a kasar Indiya, Abdulrazaq Nafi’u Abubakar, mai shekaru 27 ya samu kyautar shugaban makaranta ta kambun zinare bayan ya zama zakakurin dalibin da ya fi kowanne hazaka a karatunsa na digirin-digir da ya yi a fannin fasahar karatun Engineering a jami’ar Sharda da ke Indiya, Daily Trust ta ruwaito.

Abubakar dan asalin karamar hukumar Nasarawa ne, kuma ya kammala karatu da CGPA 9.89 bisa 10 a kasar Indiya.

Dama ya yi digirinsa na farko ne a fannin Mechatronics Engineering a jami’ar Bayero da ke Kano, kuma ya samu kyautar Ahmadu Adamu ta shekarar 2019 bayan ya kammala digiri da CGPA 4.9 bisa 5.

Bayan kammala karatunsa na digiri a shekarar 2019, an dauki nauyin karatunsa inda ya shiga cikin dalibai 370 da su ka kammala karatu da digiri mai daraja ta farko daga jihar Kano zuwa kasar Indiya don ya yi digirin-digir, karkashin gidauniyar cigaban Kwankwasiyya.

Bayan an tambaye shi yadda ya samu wadannan tarin nasarorin, ya ce da taimakon malamansa wadanda su ka taimaka masa da shawarwari ya ci nasarorin.

Kamar yadda ya shaida:

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe