33.7 C
Abuja
Wednesday, March 29, 2023

Hotunan kafin aure na dan gidan El-Rufai ya jawo hankalin mutane da dama a shafukan sadarwa

LabaraiHotunan kafin aure na dan gidan El-Rufai ya jawo hankalin mutane da dama a shafukan sadarwa
  • Dan gidan gwamnan jihar Kaduna, Bashir El-Rufai, ya wallafa hotunan kafin aure da ya dauka da masoyiyarsa, Halima Nwakaego Kazaure
  • Saboda akwai sunan Igbo a cikin sunan budurwar tashi ya sanya mutane suka yi ta kace-nace akan wadannan hotuna
  • Wasu na ganin hakan a matsayin kokari na ganin an samu goyon baya daga yankin kudancin Najeriya, wasu kuwa na ganin irin wannan aure zai taimaka matuka wajen hada kan Najeriya

A yanzu haka dai kararrawa na ta bugawa a gidan gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, kan auren dan shi Bashir da zukekiyar budurwarshi Halima.

Bayan ya bayyana shirin aurensu da masoyiyarsa, Halima Nwakaego Kazaure, Bashir ya wallafa hotunan kafin aurensu da suka dauka da masoyiyar tashi.

Ya wallafa hotunan a shafinsa na Twitter, inda ya ce: “My Nwakaego $ I,” ma’ana “Ni da Nwakaego di ta.”

KU KARANTA: Na hannun daman Ganduje ya rabawa matasan yankinsa jakuna domin su dogara da kansu

Haka ita ma budurwar ta shi, Halima, ta wallafa wasu daga cikin hotunan nasu a shafinta, daya a cikin kayan gargajiya, dayan kuma a cikin kayan zamani, inda a kasa ta rubutu dan takaitaccen tarihin soyayyarsu.

Ta bayyana cewa sun fara soyayya daga haduwa a shafin yanar gizo, inda har ta kawo wannan matsayin. Da take yi masa kirari, ta ce shi kadai ne namiji da zai iya hakuri da ita, inda ta ce shine rabin rayuwarta.

https://twitter.com/hungrynggirl/status/1327369456499175426?ref_src=twsrc%5Etfw%7Ctwcamp%5Etweetembed%7Ctwterm%5E1327369456499175426%7Ctwgr%5E&ref_url=https%3A%2F%2Fwww.legit.ng%2F1383741-prewedding-photos-bashir-el-rufai-nwakaegos-catch-nigerians-attention.html

KU KARANTA: Kotu ta bawa ‘yan sanda umarnin bincikar Aisha Yesufu kan iza wutar zanga-zangar EndSARS

Saboda masoyiyar Bashir na da sunan Igbo a cikin sunanta, hakan ya jawo kace-nace matuka a shafukan sadarwa. Wasu sunyi Allah wadai dashi da ya auri Igbo, inda wasu kuma suka bayyana hakan a matsayin wata hanya ta siyasa. Wasu kuwa sun nuna goyon bayan su dari-bisa-dari kan hakan, inda suke ganin hakan zai taimaka wajen hada kan kasa baki daya.

Ga dai wasu daga cikin maganganu da mutane suka yi ta faman yi a shafukan sadarwa na Twitter:

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/laabarunhausa/

Twitterhttps://www.twitter.com/labarunhausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: labarunhausaa@gmail.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe