25.1 C
Abuja
Saturday, January 28, 2023

Maganar Ahmed Lawan ta tabbata an cafke wasu ‘yan bindiga da suka yi tuban muzuru a Katsina

LabaraiMaganar Ahmed Lawan ta tabbata an cafke wasu 'yan bindiga da suka yi tuban muzuru a Katsina

A makonnin da suka gabata ne shugaban majalisar dattawa na kasa Sanata Ahmed Lawan yaa bada sanarwar cewa dole ‘yan Najeriya su sanya ido kan ‘yan bindiga da ‘yan Boko Haram da suka ce sun ajiye makamansu sun tuba.

Hukumar ‘yan sandan jihar Katsina ta samu nasarar kama wasu mutane a jihar da laifin yaudara da kuma satar kayan al’umma akan cewa suna aiki ne da ofishin mai ba gwamna shawara a fannin tsaro.

Mutanen wadanda suka kasance tsofaffin ‘yan ta’adda ne da suka tuba kuma suka nuna cewa za su bada hadin kai wajen taimakawa gwamnatin jihar shawo kan matsalar rashin tsaro a jihar, an bayyana sunayen su kamar haka, Usman wanda yake da shekaru 50 a duniya dake zaune a kauyen Ganuwa dake cikin karamar hukumar Charanchi; Abdullahi Mai-Rafi dan shekara 43 wanda ke zaune a kofar Marusa Low-Cost; da kuma Abbas Haruna mai shekaru 34, mazaunin unguwwar Filin Polo.

Ahmed Lawan
Shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Gambo Isah ne ya gurfanar da masu laifin tare da wasu masu laifuka daban-daban da aka kama a fadin jihar.

A bayanin kakakin rundunar, ya bayyana cewa, mutanen da ake zargin sun shiga cikin dajin Danmarke wanda ke cikin karamar hukumar Ingawa a ranar 11 ga watan Agusta, cikin wata mota mai kirar Camry wacce ke da lamba (DE 631 LED).

Bayan shigar su dajin sun iske wani mutumi mai suna Alhaji Gide Suleiman, wanda ya fito daga karamar hukumar Malumfashi a cikin rugarshi, inda suka yi masa gargadi cewar suna aiki da ofishin mai bawa gwamnan jihar shawara a fannin tsaro.

Masu laifin sun bayyanawa mutumin cewa akwai wani mai suna Sa’idu da ya sace shanun Lawal, don haka ya nemo inda Lawal yake ko kuma ya kawo shanaye guda dari (100).

Bayan shafe lokaci mai tsawo ana muhawara tsakaninsu, wadanda ake tuhumar sun damfari Alhaji Gide shanaye guda ashirin, wadanda aka yi musu kudi sama da naira miliyan bakwai da dubu dari biyar (N7.5m), inda suka sanar da mutumin cewa za su mayarwa da Lawal din da aka sacewa shanaye.

Bayan haka kuma sun yiwa Alhaji Gide kankat, inda suka kwace masa wayoyinsa na hannu guda hudu da kuma tsabar kudi har naira dubu arba’inn (N40,000).

Daga baya kuma Abdullahi Mai Rafi ya sake yunkurin yaudarar Alhaji Gidee wasu shanaye guda ashirin, sai dai kuma a wannan karon dubun shi ta cika aka samu nasarar cafke shi.

Bayan gabatar da kwakkwaran bincike, wadanda ake zargin sun amsa laifukansu baki daya, inda kuma suka tabbatar da cewa sun sayar da wadannan shanaye a kasuwar Dankama.

A sanya ido sosai, zai iya yiwuwa tuban muzuru ‘Yan Boko Haram ke yi – Sanata Ahmed Lawan

Idan ba a manta ba a ranar 24 ga watan Agusta ne muka kawo muku rahoton cewa, shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan ya ce dole ‘yan Najeriya su sanya ido wajen karbar ‘yan Boko Haram da suka nuna cewa sun ajiye makamai sun tuba kuma suna neman gafara.

Da yake magana da manema labarai bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa ranar Litinin, Sanatan ya ce dole a sanya ido don tabbatar da cewa wadanda suka tuba din tuban gaskiya suka yi.

Helkwatar tsaro ta kasa ta ce sama da mutum 1,000 ne ‘yan Boko Haram din da suka hada manyan kwamandojin su da masu hada musu bama-bamai suka mika wuya ga rundunonin sojin Najeriya dake yankin Arewa maso Gabas.

Mutane da yawa sun nuna rashin goyon bayansu akan kokarin da gwamnatin tarayya take na koyawa tubabbun mayakan sana’a ta kuma sanya su cigaba da yawo cikin al’umma.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Katsina Post

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe