A karshe dai an sulhunta rigimar dake tsakanin Ummi Rahab da wasu daga cikin yaran jarumi Adam A Zango, wanda rigimar ta samo asali ne bayan ‘yar hatsaniyar da ta faru tsakanin Adam A Zango da Ummi Rahab din har ta yi barazanar tona masa asiri, inda hakan ya fusata masoyan sa da yaran sa, hakan ya sanya suka dinga yi mata martani wasu a rubuce, wasu cikin sautin murya, wasu kuma aa bidiyo.
Sai dai cikin wadanda martaninsu yafi tada kura akwai Abdul Babulaye da Umar Bigshow, indaa Umar ya yi rubutu a kasan bidiyon Ummi, shi kuma Abdul ya yi bidiyo na raddi ga Ummi, gami da kara bayyana abin da ya sani dake tsakanin Ummi Rahab din da mai gidansa.
Maganganun Abdul da Umar ba su yiwa Ummi daa masoyanta dadi ba, inda hakan ya sa ta shigar da kara ga hukumar ‘yan sanda bisa zargin su da yi mata barazana da bata suna, da kuma sauran abubuwa da take tuhumar su da shi, inda a karshe aka gayyace su aka kuma sulhunta.
A karshe dai hukuma ta saka Abdul da Umar suka yi bidiyo suka wallafa a shafukansu su dan bayyanawa duniya sabani aka samu, amma yanzu komai ya wuce kuma suna masu bada hakuri ga Ummi Rahab.
Da Tashar YouTube ta Tsakar Gida ta nemi karin bayani a wajen dann uwan Ummi Rahab, wato Yasir M Ahmad, ya bayyana musu cewa suma a nasu bangaren komai ya riga ya wuce, kuma sun yafewa kowa, da suka tambayesu akan ko yafiyar ta shafi mai gidan nasu wato Adam A Zango, Yasir ya ce ba zai cee komai akan wannan batu ba tukunna, saboda yanzu magana ce ake ta abinda dake tsakanin Ummi Rahab da Abdul da kuma Umar, kuma hukuma ta shiga tayi musu iyaka, amma batun Ummi Rahab da Adam A Zango, wani abu ne kuma daban.

A gaggauta mayar da Ummi Rahab Saudiyya – Mai rajin kare hakkin dan Adam ya kaiwa kwamishinan ‘yan sanda koke
A wani sabon koke da fitaccen mai rajin kare hakkin dan Adam, Muhammad Lawan Gusau ya kai ga kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kaduna, kan wani hoton takardar koken da Ummi Rahab ta kai ga hukumar ‘yan sandan farin kaya na CID, wacce ke zargin cewa Adam A Zango na bata mata suna.
Muhammad Lawan ya yiwa kwamishinan ‘yan sandan fashin baki kan koken da Ummi ta kai, kana ya nemi a mayar da ita kasarta ta haihuwa kamar yadda Yasir ya bayyana cewa ‘yar Najeriya ba ce.
Muhammad Lawan ya aikawa da Tashar YouTube ta Tsakar Gida, wannan koke nasa, bayan ya aikawa kwamishinan ‘yan sanda na Kadduna, ya kuma aika wani kwafin ga mataimakin kwamishina na CID, biyo bayan sakon da ke yawo da kuma maganganun da dan uwanta Yasir ya yi, ga dai yadda koken ya ke.
Takardar koken mai dauke da kwanan watan 25 ga watan Agustan shekarar 2021, an aikata ne ga babban kwamishinan ‘yan sanda na hukumar ‘yan sandan jihar Kaduna, ya fara da cewa.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Source: Tashar Tsakar Gida
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com