34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Atra: ‘Yar kasar Saudiyya da take noma da kanta don ta tallafawa iyayenta

LabaraiAtra: 'Yar kasar Saudiyya da take noma da kanta don ta tallafawa iyayenta

Wata budurwa ‘yar shekara 19 a duuniya mai suna Atra, ‘yar asalin kasar Saudiyya ta zage danttse wajen yin noma don ta tallafawa iyayenta, ta ajiye karatunta da komai don ta kula da iyayen nata wadanda suka tsufa.

Mun sha jin labari cewa ‘ya’ya maza sune suke tallafawa iyayeynsu idan suka tsufa. Ana tarairayar ‘ya’ya maza a kasashe daban-daban a duniya yayin da maza kuma ake yi musu wani kallo daban.

Sai dai kuma, mata a ‘yan kwanakin nan suna zama abin kwatance haka kuma baza a ce karya bane idan aka matan kasar Saudiyya suna kan sahun gaba.

Wata yarinya ‘yar kasar Saudiyya ta zama abin kwatance yayin da take aiki tukuru wajen ganin ta tallafawa iyayenta da suka tsufa. Wannan labarin Atra ne, yarinya ‘yar shekara 19, wacce ta ajiye karatunta da kuruciyarta don ta tallafawa iyayenta.

Saudiyya

Ta bayyana cewa tana aji shida na sakandare ta fara koyon yadda ake tuka motar noma. Ta ce sai ta gama aikin gida baki daya kafin ta fita taje tayi noma. Ita kadai ce take iya samar musu da abinci a gidan.

Ta shafe shekaru tana fita bayan gari, tun tana yarinya karama take fita da kayanta masu kyau taje ta zage dantse domin samar da abinci ga iyayen nata.

Atra 1

Ta ce mahaifinta yayi mata komai na rayuwa, shine abokinta, mahaifinta, dan uwa kuma wanda yake tallafa mata a duk lokacin da take nema. Wani ma’aikacin gidan talabijin na MBC, Mohammad Al Jumairi shine ya bayyanna labarin Atra.

Yaro dan shekara 14 Musulmi da ya zama Farfesa mafi kankanta a duniya

Mun saba ganin yara ‘yan shekara 14 suna tafiya makaranta, amma kun san wani abu wannan yaron yayi da ya sanya ya zama farfesa a jami’ar Leicester dake kasar Birtanniya?

Manyan Dalilan da su ke sa miskilan maza farin jini da tasiri a zuciyoyin ‘yan mata

Tare da ilimin lissafi mai ban mamaki, Yasha Ashley mai shekaru 14 a duniya ya zama farfesa mafi karancin shekaru a duniya. Yasha na koyarwa a jami’ar Leicester yayin da kuma yake cigaba da karatun sa.

Yayin da yara da dama kamar sa ke wasa a lokutan da suka samu babu abinda suke yi, wannan karamin yaro a nashi bangaren ya dage wajen taimakawa mutane da ilimin da Allah ya bashi.

Mahaifin Yasha, Moussa Ashley, shine yake kai shi jami’ar a kowacce rana. Ya nuna yadda yake alfahari da dan nashi, wanda a koda yaushe yake matukar son lissafi. Ganin yadda danshi yake da ilimin lissafi sosai ya sanya ya kai sunanshi jami’a.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Life In Saudi Arabia

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe