27.1 C
Abuja
Saturday, October 1, 2022

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata...

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin...

Juyin Mulki: Sojoji Sun Hanɓarar da Shugaban Ƙasa Mai Ci

Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin...

Muna rokon Allah ya yi mana maganin Buhari idan har ba zai iya kare rayukan al’umma ba – Sheikh Nuru Khalid

LabaraiMuna rokon Allah ya yi mana maganin Buhari idan har ba zai iya kare rayukan al'umma ba - Sheikh Nuru Khalid

Babban Limamin Masallacin Apo Legislative, Sheikh Muhammad Nuru Khalid, ya caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari akan kasa tabuka komai da yake wajen kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.

Da yake bayani a wajen hudubar ranar Juma’a, Limamin ya ce shugaban kasar ya iske Najeriya a hade kasa guda daya, amma ya kyale ‘yan bindiga suna rike da wani bangare na kasar a yanzu.

Ku je ku sanar da shugaban kasa cewa a karkashin gwamnatinsa akwai wasu tsirarun mutane da suka zama barazana ga mazauna wasu wurare, sun bukaci su hada kudi ko kuma su kai musu hari, kuma anyi haka a jihar Zamfara, cewar Sheikh Khalid.

Kuma sun hada kudin, har sun sanar da BBC cewar za su biya ‘yan bindigar wannan kudi a yau Juma’a.

Ku gayawa shugaban kasar akwai kasar da muke da ita Najeriya, da kuma wacce bamu sani ba wacce ‘yan bindiga suke da iko da ita yanzu.

Ko dai shugaban kasar ya dawo da kasar kamar yadda ya same ta, ko kuma muna yi masa addu’ar Allah yayi mana maganinsa.

Wannan budadden sako ne kowa ya gani a duniya. Na yadda da duk wani abu da za ayi mini, kuma na shirya fuskantar duk wani hukunci da za ayi mini kan kira ga hadin kan Najeriya.

Ya mai girma shugaban kasa bama so muji ana fitar da rahoton kashe mutane a karkashin mulkin ka. Ba mu son jin labarin abin kunya ga sojojin mu, kamar wanda aka fitar makon nan na cewa an kai musu hari har gidansu.

Muna da bidiyon ka, inda kake cewa suna da kwarewa wajen kawo karshen matsala kowacce iri ce a kasar nan. Ka ce idan aka zabeka zaka basu duka goyon bayan da za su kawo karshen ta’addanci cikin kankakin lokaci.

Ya shugaban kasa alkawari kaya ne. Idan har baka da masu baka shawara kan yadda zaka kawo karshen wannan lamari, mu mun shirya mu sanar da kai. Muna addu’ar Allah ya baka ikon cika wannan alkawari daka dauka idan kana so ka cika, idan kuma baka so ka cika muna rokon Allah ya raba mu da kai.

Sheikh Muhammad Nuru Khalid
Sheikh Muhammad Nuru Khalid

‘Yan Najeriya ba su zabeka don ka ke yi musu magana ta bakin mataimaka ba – Ndume ga Buhari

Haka shi ma shugaban kwamitin sojojin Najeriya na majalisar dattawa, Sanata Mohammed Ali Ndume mai wakiltar jihar Borno ta Kudu ya koka akan yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yiwa ‘yan Najeriya magana ta bakin mataimaka a lokutan da ya kamata ya fito kowa yaji muryar shi.

Ndume wanda ya yi magana da manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, 26 ga watan Agusta, a lokacin da yake mayar da martani akan harin da aka kai Kwalejin horar da sojoji ta Najeriya (NDA) ya ce shirun da shugaban kasar ya yi dangane da irin wannan babbar matsala bai da fa’ida, rahoton Daily Trust.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe