23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Yazid Surajo: Matashin saurayi dake da digiri na biyu amma yake sana’ar jari bola

LabaraiYazid Surajo: Matashin saurayi dake da digiri na biyu amma yake sana'ar jari bola

Matashin da aka haife shi a garin Karofi cikin karamar hukumar Dutsinma dake jihar Katsina, Yazid Surajo yana da kwalin digiri na biyu a fannin karatun cigaba daga jami’ar Bayero dake Kano, yanzu yana aikin jari bola a birnin Legas.

Yazid Surajo ya yi karatun Firamare a makarantar Firamare ta Karofi Model daga shekarar 1996 zuwa 2002. Daga nan ya wuce makarantar sakandare ta GSSS, Karofi daga shekarar 2002 zuwa 2008, Daily Trust ta bayyana haka a wata hira da tayi dashi a ranar Asabar 17 ga watan Afrilu.

A shekarar 2010, ya wuce jami’ar Umar Musa Yar’adua, dake Katsina, inda ya yi karatu a fannin tarihi, ya kammala a shekarar 2010.

Sai dai kuma, a lokacin da yake makaranta, Yazid Surajo ya rasa mahaifinsa wanda a lokacin Sufeto ne na ‘yan sanda a shekarar 2010. Rayuwa ta yi wahala a gareshi saboda iyalan suna ta fama don ganin gwamnati ta sauke nauyin mamacin.

A cewar Surajo, sai da suka shafe shekara 10 kafin hukumar ‘yan sanda ta kasa ta basu naira miliyan uku da rabi (N3.5m), wanda hakan rabi ne na abinda ya kamata a ba su na mamacin.

Mun sha wahala sosai wajen ganin mun samu kudin nan akan lokaci sabooda wahalar rayuwa da muke ciki. An damfare mu sosai kafin mu samu a biya mu wannan kudi a karshe, cewar Surajo.

Rayuwa bayan makaranta

Bayan kammala digirin shi na farko, da kuma bautar kasa a jihar Osun, Surajo ya fara tunanin hanyar da zai dauka ta rayuwa.

Yazid Surajo
Yazid Surajo

Cikin sa’a sai aka zabe shi cikin ma’aikaatan N-Power, inda aka biyan shi naira dubu talatin a wata.

Bayan ya kammala aikin N-Power, Yazid Surajo ya tafi jihar Legas neman aiki. bayan cika ayyuka da dama bai samu ba, matashin saurayin ya yanke shawarar shiga harkar jari bola.

Ya ce:

Abu ne da kowa ya sani, idan har kana so ka zama wani abu a rayuwa, dole ne sai kayi aiki tukuru. A lokacin dana kammala bautar kasa a shekarar 2016, na yanke shawarar ba zan zauna babu aikin yi ba.

Da yawa daga cikin abokanai na da muka taso, suna zuwa jihar Legas, saboda haka nima banyi kasa a gwiwa ba wajen bin su. Wasu sun ce irin wannan aikin bai kamace ni ba, saboda yana bukatar karfi da wahala. Wadanda kuma suka sanni da kuma abubuwan da zanyi sun riga sun san cewa zan iya jure kowanne wahala.

Yadda aikin jari bola yake

Yazid Surajo ya ce shi da wasu mutane kusan su 70, suna aiki a karkashin wani mai suna Dandogo. Dandogo yanaa basu kudi a kowacce rana suje su sayo masa kayan bola.

Ya ce:

Wasu ana iya basu N7,000, wasu N10,000, wasu ma har N30,000 ana iya basu ya danganta da yanayin. Bayan mun karbi kudin kowa zaii dauki baron shi ya tafi neman kayan bola.

Idan kaci karo da kayan da yafi karfin kudin da aka baka, sai ka kira Dandogo, shi zai turo kudi, da yamma tayi kowa zai koma ya kai kayan da ya siyo, za a gwada nauyin kayan, shugaban mu zai dauki kudin shi sai ya bawa kowa ribar shi. Wannan shine yadda muke yin kasuwancin mu a kowacce rana.

Komawa karatun digiri na biyu

A shekarar 2018, Yazid Surajo ya samu gurbin karatu na digiri na biyu a jami’ar Bayero dake Kano.

Don biyan kudin makarantar sai da ya sayar da filin shi, tare da aikin da yake yi na jari bola haka ya samu ya kammala karatun shi.

Burin Yazid Surajo na gaba

Surajo ya ce yana so ya zamanantar da sana’ar jari bola idan ya samu jarin da yakee bukata. A cewar shi:

Zan yiwa kamfani na rijista, sannan kuma zan dauki ma’aikata. Zan koyar da su akan irin kayan da za su iya sayowa da kuma irin mutanen da za su dinga sayen kaya a wajen su.

Haka kuma zanyi amfani da kafar sadarwa wajen kiran matasa da su tashi su fara sana’a ko yaya take. Haka kuma ina kira gare su dasu nesanta kansu daga aikata kowanne irin aikin ta’addanci irin su, damfarar yanar gizo, fashi da makami, garkuwa da mutane, da dai sauran ayyukan ta’addanci.

A shafinsa na Facebook, Surajo ya wallafa hoton shi dauke da kayan bola da kumaa takardun shi na digiri, inda ya ce:

Zai fi mutum ya mutu yana neman na kai, da ka zauna kana dogaro da wani. gwanda na shiga cikin datti da wahala na nemo abinci dana zauna ina yawo da yunwa a ciki. Duka a kasar da ba a dauki masu hazaka da muhimmanci ba.

Kyakkyawar budurwa da ta kammala digiri ta rungumi sana’ar sayar da cin-cin a titi

Wata matashiyar budurwa ‘yar shekara 23, mai suna Chizitere Daniel Vivian, ta bayyana cewa rashin aikin yi ne ya sakata fara sana’ar toya cin-cin ta kuma dauka ta sayar akan tituna.

Dalibar wacce ta karanci fannin ilimin yanayi da tsare-tsare, a jami’ar jihar Legas, ta ba wa ‘yan Najeriya shawarar su dai na dogaro da kwalin digiri, ko kuma su tsaya jiran gwamnati ta basu aiki.

Matashiyar ta bayyana hakan ne a yayin zantawar ta da wakilin legit.ng Adeoye Adewunmi a ranar litinin 16 ga Agusta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Daily Trust

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe