23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

A karon farko Abba Kyari ya bayyana a shafukan sadarwa jim kadan bayan an kammala bincike a kan shi

LabaraiA karon farko Abba Kyari ya bayyana a shafukan sadarwa jim kadan bayan an kammala bincike a kan shi

A ranar 26 ga watan Agusta ne mataimakin kwamishinan ‘yan sanda (DCP) Abba Kyari, ya bayyana a shafin sadarwa bayan shafe makonni biyu ba aji duriyar shi ba, tun bayan zargin shi da ake yi kan badakalar Abbas Ramon (Hushpuppi) ta dala miliyan daya.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa’ Kyari wanda aka dakatar daga aiki, ba a sake jin duriyar shi ba a shafukan sadarwa, bayan rubdugu da aka yi masa a shafinsa na Facebook a ranar 4 ga watan Agusta, wanda daga baya ya goge.

Jaridar Labarun Hausa ta gano cewa hazikin dan sandan dan asalin jihar Borno ya hau shafinsa na Facebook mai dauke da mabiya sama da mutum 450,000 a ranar Alhamis 26 ga watan Agusta.

A yadda rahoton ya nuna, Kyari ya wallafa wani matsakaicin bidiyo mai tsawon dakika 21, na TikTok wanda wata Sandra Tobacco ta sanya, wanda aka nuno a cikin fara’a da annushuwa yana cewa wani dake tura shi a baro “is very crazy wallahi”.

Kotun kasar Amurka ta bada umarnin a kamo mata mataimakin kwamishinan ‘yan Sandan Najeriya, Abba Kyari, bisa zargin hannu a cikin harkallar fitaccen dan damfarar nan na yanar gizo, Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Alkalin kotun na jihar California Ortis Wright, shine ya bawa hukumar FBI umarnin kamo Abba Kyari a kuma gurfanar da shi a gaban kotun bisa hannu a cikin damfarar ta miliyoyin daloli da aka yi.

An kama Abbas ne dai a hadaddiyar Daular Laraba a watan Yulin shekarar 2020, kuma ya amsa laifin shi na damfarar a kasar Amurka makon da ya gabata.

FBI ta bayyana cewa Abbas da Abba Kyari na da kusanci da juna, saboda haka duka ana zargin su da hannu a wannan damfara.

A rahoton da jaridar People’s Gazette ta wallafa a shafinta, ta bayyanaa cewa tun ranar 12 ga watan Fabrairu ne aka bada umarnin kamo Abba Kyari, haka kumaa a ranar 29 ga watan Afrilun shekarar 2021, an sake bada sammacin kamo shi.

Lauyoyin Arewa 31 sun sha alwashin tsayawa Abba Kyari a kotu

Akalla lauyoyi 31 ne suka nuna sha’awarsu wajen kare mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari, wanda aaka dakatar daga aikin sakamakon zargin shi da ake yi da hannu a badakalar dan damfara, Ramon Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Barista Baffa Salisu, wanda ya yi magana a madadin kungiyar lauyoyin wadanda suka fito daga jihohi 19 na Arewacin Najeriya, ya bayyana haka a ranar Laraba a cikin wata sanarwar da ya fitar a Abuja.

Lauyoyin sun ce shawarar da suka yanke ta bawa Kyari goyon baya a shari’ar shi kyauta, ta biyo bayan kiran da kungiyoyin Arewa suka yi kwanan nan wajen ganin an kare masa hakkinsa, biyo bayan tuhumar da kotun Amurka ta ke yi masa.

A cewar shi, akwai ka’idoji da dama da hukumar FBI ta karya wajen kokarin kama Abba Kyari, hukumar na bukataar tsohon kwamandan rundunar ‘yan sandan ya fuskanci hukunci akan tuhumar da ake yi masa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Tashar Tsakar Gida

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe