29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

‘Yan Najeriya ba su zabeka don ka ke yi musu magana ta bakin mataimaka ba – Ndume ga Buhari

Labarai'Yan Najeriya ba su zabeka don ka ke yi musu magana ta bakin mataimaka ba - Ndume ga Buhari

Shugaban kwamitin sojojin Najeriya na majalisar dattawa, Sanata Mohammed Ali Ndume mai wakiltar jihar Borno ta Kudu ya koka akan yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yiwa ‘yan Najeriya magana ta bakin mataimaka a lokutan da ya kamata ya fito kowa yaji muryar shi.

Ndume wanda ya yi magana da manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, 26 ga watan Agusta, a lokacin da yake mayar da martani akan harin da aka kai Kwalejin horar da sojoji ta Najeriya (NDA) ya ce shirun da shugaban kasar ya yi dangane da irin wannan babbar matsala bai da fa’ida, rahoton Daily Trust.

Ya ce:

Kawai na damu ne yadda shugaban kasar baya yiwa ‘yan Najeriya magana. Yin shiru a matsala irin wannan ba abu ne mai fa’ida ba.

Sanatan Arewan wanda ke a babbar jam’iyya mai mulki ta APC, ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi koyi da shugaban kasar Amurka, Joe Biden wanda yake magana da ‘yan kasar Amurka a kowacce rana dangane da rikicin Afghanistan, cewar jaridar Nigerian Tribune.

Ya bayyana cewa yin magana da ‘yan Najeriya a lokaci irin wannan kuma ya kai ziyara wajen zai taimaka matuka wajen karawa ‘yan Najeriya karfin gwiwa, zai kuma cire tsoro a zukatan ‘yan Najeriya.

Ndume ya ce:

Irin wannan mataki zai saka tsoro ya fita a zukatan mutane. Ba wai iya bawa jami’an tsaro kayan aiki bane kawai abinda zai yi ba, shugaban kasar dole ya dauki mataki akan irin wannan lamuran.

Haka kuma dole ya dinga kai ziyara wuraren da irin wadannan abubuwa suke faruwa domin kawo mafita akan lamarin.

Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin kai hari NDA

A wani rahoto na daban kuma, mai magana da yawun shugaban kasa, ya ce harin da aka kai kwalejin horar da sojojin ta Kaduna, anyi shi ne don kunyata gwamnatin shugaban kasa Buhari.

Wasu ‘yan bindiga da har yanzu ba a san ko su waye ba sun kai hari NDA a ranar Talata, 24 ga watan Agusta, inda suka kashe sojoji guda biyu suka kuma yi awon gaba da Manjo daya.

Wannan lamari ya kawo matsala sosai akan cigaba da samun matsalar tsaro da ake yi a kasar.

Da yake magana dangane da lamarin a ranar Laraba, 25 ga watan Agusta, Shehu ya ce fadar shugaban kasa tana bukatar hukumar tsaro tayi bincike mai zurfi kan lamarin.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Tashar Tsakar Gida

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe