29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Za mu bawa Ummi Rahab dama ta fito ta yiwa duniya bayani kan Adam A Zango – Yasir

LabaraiKannywoodZa mu bawa Ummi Rahab dama ta fito ta yiwa duniya bayani kan Adam A Zango - Yasir

Dan uwa a wajen Ummi Rahab ko kuma muce marikinta Yasir M Ahmad ya yi wani rubutu a shafin sa dake nuna shima yana kan ra’ayi irin na Ali Artwork wato sai Adam A Zango ya fito ya janye kalaman sa akan Ummi din a kafofin sada zumunta kafin su yadda ayi sulhu, inda ya nuna hoto na kan wayarshi da kuma kira da Adam A Zango ya yi masa bai daga ba gami da rubuta cewa:

Ni Yasir Dan Uwan Ummi Rahab ni kaina na yarda da sulhu saboda mun san cewa sulhu alkhari ne amma mu abunda muke bukata shine kaje Social Media inda kayi Magana akan Ummi wanda bata jiba bata gani ba kaje ka janye kalamanka duniya tasan gaskiyar cewa @ummirahabofficial mata Maka Butulci ba. 🙏 Sannan Maganar Film din Farin Wata mu muka cire Ummi saboda wasu dalilai?

Da yake yiwaa Tashar YouTube ta Tsakar Gida karin bayani dangane da wannan sako nasa, Yasir ya bayyana cewa su fa a shirye suke da ayi sulhu wannan maganar ta wuce, amma ba za su lamunta da sulhun karkashin kasa ba, lallai sai Adam A Zango ya janye kalaman sa a kafafen sada zumunta, saboda ya zuwa yanzu ya kasa karyata bidiyon da ya yi na cewar soyayya suka yi da Ummi.

Yasir ya ce idan Adam Zango ya gaza yin haka nan da kwana biyu zai bawa Ummi dama tayi magana da bakin ta a kafar sadarwa ta zamani don ta bayar da labarin soyayyar su da Adam A Zango.

To sai dai kuma a wani sautin kiran waya da muka samu, ya nuna cewa a karshe dai Yasir ya daga wayar Adam A Zango, har ma sunyi magana ta tsawon mintuna biyar da wasu ‘yan dakiku, duk da dai cewa ba a kai ga matsaya a wayar ta su ba, amma dai mun jiyo muryar shi Yasir yana bawa jarumin hakuri akan lamarin, ga dai yadda wayar ta su ta kasance:

A gaggauta mayar da Ummi Rahab Saudiyya – Mai rajin kare hakkin dan Adam ya kaiwa kwamishinan ‘yan sanda koke

A wani sabon koke da fitaccen mai rajin kare hakkin dan Adam, Muhammad Lawan Gusau ya kai ga kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kaduna, kan wani hoton takardar koken da Ummi Rahab ta kai ga hukumar ‘yan sandan farin kaya na CID, wacce ke zargin cewa Adam A Zango na bata mata suna.

Muhammad Lawan ya yiwa kwamishinan ‘yan sandan fashin baki kan koken da Ummi ta kai, kana ya nemi a mayar da ita kasarta ta haihuwa kamar yadda Yasir ya bayyana cewa ‘yar Najeriya ba ce.

Muhammad Lawan ya aikawa da Tashar YouTube ta Tsakar Gida, wannan koke nasa, bayan ya aikawa kwamishinan ‘yan sanda na Kadduna, ya kuma aika wani kwafin ga mataimakin kwamishina na CID, biyo bayan sakon da ke yawo da kuma maganganun da dan uwanta Yasir ya yi, ga dai yadda koken ya ke.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Tashar Tsakar Gida

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe