23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

A gaggauta mayar da Ummi Rahab Saudiyya – Mai rajin kare hakkin dan Adam ya kaiwa kwamishinan ‘yan sanda koke

LabaraiKannywoodA gaggauta mayar da Ummi Rahab Saudiyya - Mai rajin kare hakkin dan Adam ya kaiwa kwamishinan 'yan sanda koke

A wani sabon koke da fitaccen mai rajin kare hakkin dan Adam, Muhammad Lawan Gusau ya kai ga kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kaduna, kan wani hoton takardar koken da Ummi Rahab ta kai ga hukumar ‘yan sandan farin kaya na CID, wacce ke zargin cewa Adam A Zango na bata mata suna.

Muhammad Lawan ya yiwa kwamishinan ‘yan sandan fashin baki kan koken da Ummi ta kai, kana ya nemi a mayar da ita kasarta ta haihuwa kamar yadda Yasir ya bayyana cewa ‘yar Najeriya ba ce.

Muhammad Lawan ya aikawa da Tashar YouTube ta Tsakar Gida, wannan koke nasa, bayan ya aikawa kwamishinan ‘yan sanda na Kadduna, ya kuma aika wani kwafin ga mataimakin kwamishina na CID, biyo bayan sakon da ke yawo da kuma maganganun da dan uwanta Yasir ya yi, ga dai yadda koken ya ke.

Takardar koken mai dauke da kwanan watan 25 ga watan Agustan shekarar 2021, an aikata ne ga babban kwamishinan ‘yan sanda na hukumar ‘yan sandan jihar Kaduna, ya fara da cewa:

Zuwa ga babban kwamishina,

Fayyacewa akan wasu abubuwa dangane da takardar koke na yin zamba cikin aminci da bataa suna wanda Ummi Rahab tayi akan Adam A Zango.

Tare da ladabi da girmamawa ranka shi dade, zanyi amfani da wannan dama in bada karin bayani dangane abubuwan da ke faruwa a kafafen sadarwa na zamani.

Mai karar mai suna Ummi Rahab, wacce ke zaune a titin Tishama jihar Kano, ta shigar da takardar koke akan zamba cikin aminci da bata suna akan Adam A Zango, ina so in kara da cewa anyi hira da shi Adam A Zango a kafar sadarwa ta BBC, kuma babu inda yayi kalaman batanci, tunda ta kasance karkashin kulawarsaa kafin sabanin dake tsakaninsu yanzu.

Tuni mun shigar da ta mu takardar don neman sasanci da bincike ga hukumar kula da fataucin yara dake Abuja dangane da wannan sabani dake tsakaninsu, ga kwafin takardar don karin bayani.

A karshe rankaa shi dade zanyi amfani da wannan damar domin in bada goyon bayana da hadin kai a lokacin bincike, a fahimta ta Ummi Rahab ba ta fahimci hirar da aka yi da Adam A Zango ta BBC Hausa ba, shi yasa ta mayar da martani cewa idan bai daina maganganun da yake ba za ta tona masa asiri, wanda wannan furuci wani salon batanci ne ga shi Adam A Zango.

Har ila yau, doka ma za ta bincike mutanen dake rike da ita Ummi Rahab don yiwa kowa adalci, tunda ba ‘yan uwanta ko danginta bane, kuma ayyukansu ya saba a dokokin da aka tanada a kundin kare hakkin yaraa na kasa da aka tanada na shekarar 2003.

Bugu da kari a martanin da Yasir ya yi a kafar sadarwa ya ce shi yayane ga Ummi Rahab, ya fada karara cewa an kawo ta daga kasar Saudiyya ne, kuma a yanzu mutanen dake kula da ita babu alaka ta ‘yan uwantaka tsakaninsu.

Shawarata a nan shine a gaggauta mayar da itaa inda ta fito wato Saudi Arabia bayan an kammala bincike mai zurfi.

Nagode Matuka.

Naka cikin mutunci

Lawan Muhammad Gusau

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Tashar Tsakar Gida

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe