24.4 C
Abuja
Wednesday, September 28, 2022

Kyakkyawar budurwa da ta kammala digiri ta rungumi sana’ar sayar da cin-cin a titi

LabaraiKyakkyawar budurwa da ta kammala digiri ta rungumi sana'ar sayar da cin-cin a titi

Wata matashiyar budurwa ‘yar shekara 23, mai suna Chizitere Daniel Vivian, ta bayyana cewa rashin aikin yi ne ya sakata fara sana’ar toya cin-cin ta kuma dauka ta sayar akan tituna.

Dalibar wacce ta karanci fannin ilimin yanayi da tsare-tsare, a jami’ar jihar Legas, ta ba wa ‘yan Najeriya shawarar su dai na dogaro da kwalin digiri, ko kuma su tsaya jiran gwamnati ta basu aiki.

Matashiyar ta bayyana hakan ne a yayin zantawar ta da wakilin legit.ng Adeoye Adewunmi a ranar litinin 16 ga Agusta.

lady chin chin job2

Ta bayyana cewa sana’ar cin-cin tana rufa mata asiri sannan tana iya siyan abubuwan da a baya bata iya saya.

Matashiyar ta baiwa matasan Najeriya shawarar dogaro da kai da kuma hanyar da zasu samu na kansu ba tare da jiran gwamnati ta basu aiki ba.

Ta bayyana cewa:

“Ba zanyi karya ba cewa rashin aikin yi a kasar nan ne ya saka ni fara neman na kaina.
Na yanke shawarar fara sai da cin-cin ne saboda ina son harkar girke-girke sannan ina son yiwa mutane girki.“

Yanzu haka wannan kasuwancin na cigaba da bunkasa, kuma ina iya sayen duka abubuwan da nake so a lokacin dana ke so.

To shawara ta ga masu digiri ‘yan uwana da su san abinda suke so a rayuwa su tashi tsaye su nemi abinda ya fi musu, ba wai su tsaya suna jira gwamnati ta basu aikin yi ba.

Tukin Keke Napep ya fi aikin gwamnati – Cewar mai digiri da ta ajiye aikin koyarwa

Bidiyon wata matashiyar budurwa ‘yar Najeriya daga jihar Imo da take tukin keke Napep a matsayin hanyar samun kudi ya sanya mutane da dama tofa albarkacin bakin su a shafukan sadarwa.

A wani karamin karamin bidiyo da @instablo9ja ta wallafa a shafinta na Instagram, matashiyar ta bayyana cewa ta yi karatu a Jami’ar Calabar.

Aikin koyarwa bai bani kudi da yawa

An tambayi matashiyar dalilinta na ajiye aiki inda ta bayyana cewa aikin tuka adaidaita sahu (keke Napep) yafi kawo mata kudi akan aikin koyarwa da ta yi a baya, ta bayyana cewa makarantun kudi basa biyanta da kyau.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Tashar Tsakar Gida

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe