29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Ana zargin hukumar Hisbah ta kama jaruma Umma Shehu bayan ta kirasu da mazinata

LabaraiKannywoodAna zargin hukumar Hisbah ta kama jaruma Umma Shehu bayan ta kirasu da mazinata

Biyo bayan kama Sadiya Haruna da hukumar Hisba ta jihar Kano ta yi bisa zargin ta da yada bidiyon batsa da kuma kalamai na batsa da sunan tallan magani.

Jaruma Umma Shehu ta fito ta kalubalanci hukumar ta Hisbah, inda ta bayyana hakan shiga tsakanin Allah da bawan sa ne a karshe ta kare da cewa su kansu ‘yan Hisban akwai mazinata a cikin su, idan aka kureta za ta kama suna.

Sai da wannan kalamai na ta sun bata ran al’umma musammam masu kishin addini inda suke ganin a cikin maganganunta akwai karancin fahimtar addini, inda aka dinga yi mata raddi kala-kala wasu a rubuce wasu kuma suna mata bidiyo wanda hakan ya sa ta goge bidiyon daga shafinta.

Sai dai a safiyar yau muka tashi da labarin da ake yadawa a shafukan sada zumunta cewa hukumar Hisbah ta kama Umma Shehu ita ma a jihar Kaduna.

Don tabbatar da faruwar wannan lamari Tashar YouTube ta Tsakar Gida ta yi kokarin kiran lambar wayar jarumar, amma ba ta daga ba, sai dai da suka tuntubi wasu makusantan ta sun bayyana musu cewa ba gaskiya bane batun kama ta din da ake yadawa, sai dai hakan ya sanya har yanzu ba a tabbatar da lamarin ba domin kuwa ba ta daga wayarta ba har zuwa lokacin da muke kawo muku wannan rahoto.

Ba wai iya ‘yan Kano bane suka yi sharhi akan lamarin, fitaccen mai sharhi akan al’amuran yau da kullum gami da nasiha da jan hannkali a dandalin Instagram Muhammad Rabi’u Dantine, wanda aka fi sani da Young Ustaz ya yiwa Umma Shehu da Sadiya fyadar dan kadanya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Tashar Tsakar Gida

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe