29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Tukin Keke Napep ya fi aikin gwamnati – Cewar mai digiri da ta ajiye aikin koyarwa

LabaraiTukin Keke Napep ya fi aikin gwamnati - Cewar mai digiri da ta ajiye aikin koyarwa

Bidiyon wata matashiyar budurwa ‘yar Najeriya daga jihar Imo da take tukin keke Napep a matsayin hanyar samun kudi ya sanya mutane da dama tofa albarkacin bakin su a shafukan sadarwa.

A wani karamin karamin bidiyo da @instablo9ja ta wallafa a shafinta na Instagram, matashiyar ta bayyana cewa ta yi karatu a Jami’ar Calabar.

Aikin koyarwa bai bani kudi da yawa

An tambayi matashiyar dalilinta na ajiye aiki inda ta bayyana cewa aikin tuka adaidaita sahu (keke Napep) yafi kawo mata kudi akan aikin koyarwa da ta yi a baya, ta bayyana cewa makarantun kudi basa biyanta da kyau.

Ga bidiyon budurwar a kasa

Ra’ayoyin jama’a

“Wadannan masu tukin ababen hawan fa suna samun kudi, suna samun kudi fiye da masu aikin gwamnati.”

awesomehome_varieties

“Yar imo tabar yawon banza tafara tuqa keke?? Ikon Allah gaskia ya kamata a sara mata.”

mr_v.ic_official

“Kowa yana ta kokarin neman na kai…Allah ya albarkaci neman kowa.”

ms___pat

“Kudin da ake samu a tuqin keke, ko masu aikin banki basa samun rabin kudin kawai dai aikin yanada wahala ne kuma mutane suna rainashi.”

efesocialmedia

“Ni kaina saida takalmi yafi biyana sosai, Dakyau.”

veecollections

Matashi ya kama harkar noma bayan kammala digiri

A wani labari makamancin haka kuwa wani dan najeriya mai suna Ekpono Chijioke Ugbala yana fadi tashi kamar kowa domin neman abin yi bayan kammala karatunsa.

A yayin da duk kokarinsa ya tafi a banza, bai samu damar cimma wani abu a rayuwa ba, matashin ya kama harkar noman gurji hannu biyu-biyu.

A yayin da yake noman, matashin ya nuna irin kayan da ya noma daga gonar shi , inda ya burge mutane da yawa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Tashar Tsakar Gida

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe