29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Mutane ba su fargaba ana nema a zalunci marainiyar Allah – Ali Art Work ya shiga rigimar Rahab da Zango

LabaraiKannywoodMutane ba su fargaba ana nema a zalunci marainiyar Allah - Ali Art Work ya shiga rigimar Rahab da Zango

Dangane da sato-ka-sa-katsi da ke wakana tsakanin Adam A Zango da Ummi Rahab, tsohon yaron Adam A Zango, fitaccen dan barkwancin nan kuma edita, Ali Art Work ya yi kundumbala ya shiga rigimar, inda ya zama mutum daya tilo a masana’antar Kannywood da ya fito ya kare Ummi Rahab.

Ali Art Work dai ya kasance tsohon yaron Adam A Zango, wanda ya kasance dan gaba-gaba kuma dan a mutu, saboda idan ba a manta ba a farkon rikicin Adam A Zango da Ali Nuhu har sai da ya yi wasu kwanaki a hannun ‘yan sanda sakamakon zagin Ali Nuhu da ya yi dan ya ramawa Adam A Zango rashin kunyar da Rahama Sadau ta yi wa Zango.

To a wannan karon Ali ya daura damarar tsayawa bayan Ummi Rahab gami da rokon Allah kan zaluncin da yace ana so ayi ma marainiyar Allah, amma mutane basu fargaba.

A rahoton da tashar YouTube ta Tsakar Gida ta ruuwaito, duk da dai Ali Art Work bai tsaya yya kalubalanci Adam A Zango ba, ya dai fara da saka wani gajeren bidiyo nasa da Adam A Zango da jama’a suna tafi, Adam Zango kuma da takunkumi, inda ya kara da rubuta:

Ko kun gane wannan mai takunkumin? To kuje ku tambayeshi mu da shi kar ta san kar, kuma karya karyace, sannan kuma gaskiya guda daya ce.

https://www.instagram.com/p/CS2CJwilJaO/?utm_source=ig_web_copy_link

Koda ganin wannan rubutu sai aka fara yi masa tsokaci, inda ya dinga bada amsa ga duk masa tsokaci a kasan bidiyon, inda a nan ya fito da wasu maganganu dangane da sabanin dake tsakanin Ummi Rahab da Adam Zango, duk da dai bai fito karara ba, amma kowa ya fahimci sakon da yake so ya isar.

Ali Art Work ya bada amsa a kaso mafi yawa daga cikin tsokacin da aka yi masa kan wannan bidiyo, sai dai kamar yadda yake fada akwai wadanda aka zalunta a tsakaninsu Allah ya bi masa hakkin sa, in da rabon su cigaba da tafiya tare kuma Allah ya daidaita tsaakanin su, Amin.

A jiya ne dai aka wayi gari an sake rufewa Adam A Zango na Instagram mai suna officially a zango, wanda a wannan karon shine kusan karo na biyar ko na shida da aka rufe masa shafukansa, wannan an rufe shi yana da mabiya sama da dubu tamanin.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Tashar Tsakar Gida

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe