24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Wata sabuwa: Trump ya bayyana kanshi a matsayin wanda ya lashe zaben Amurka

LabaraiWata sabuwa: Trump ya bayyana kanshi a matsayin wanda ya lashe zaben Amurka
  • Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya karya dokar sanar da wanda ya lashe zaben shugabancin kasar Amurka
  • Haka kuma Trump yayi zargin cewa magudi aka tafka a zaben shugaban kasar da aka gabatar a ‘yan kwanakin nan
  • Shugaban kasar dai har yanzu na cigaba da sukar wannan zabe da aka gabatar

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana kanshi a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar Amurka, tun kafin a bayyana sakamakon zaben kamar yadda doka ta tanada.

Trump wanda ya bayyana haka a yau Asabar, 7 ga watan Nuwamba, ta shafinsa na Twitter, ya bayyana cewa ya lashe zaben da tazara mai yawan gaske.

Shugaban kasar ya ce:

“Na lashe zaben nan, da tazara mai yawa!”

Wannan rubutu da shugaban kasar yayi ya sanya kamfanin shafin sadarwa na Twitter suka yi gaggawar yin gargadi a kasa kan cewa basu goyi bayan wannan rubutu na shi ba.

KU KARANTA: Labarin kabilar Dinka da suke sadaki da shanu 100, sannan miji zai zauna bai sadu da matarsa ba tsawon shekara 2

Wannan magana ta shugaba Trump dai ta fito ne bayan yayi zargin cewa an kidaya takardun zabe na jabu a ranar zaben bayan karfe 8 na dare a ranar Talata 3 ga watan Nuwamba.

Haka kuma yayi zargin cewa abubuwa marasa kyau sun faru a daren zaben, wanda suka yi sanadiyyar canja sakamakon zaben jihar Pennsylvania da kuma wasu sauran jihohi.

Trump yace masu lura da harkokin zaben an hana su yin aikinsu da gangan, inda hakan ya jawo aka yi wannan magudi na sakamakon zaben.

KU KARANTA: Kotu ta raba ma’aurata da suka shekara 32 tare bayan an gano mijin bai biya sadaki ba

A yau ne dai aka bayyana cewa dan takarar shugaban kasar Amurka na jam’iyyar Democrats, Joe Biden da mataimakiyarshi Kamala Harris sun lashe zaben shugabancin kasar ta Amurka, inda Biden ya bawa shugaba Donald Trump tazara mai yawan gaske a sakamakon zaben.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/laabarunhausa/

Twitterhttps://www.twitter.com/labarunhausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: labarunhausaa@gmail.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe